Arsenal ta tabbatar da sayen dan wasan tsakiyar Ingila, Declan Rice daga West Ham kan kudi fam miliyan 100 da kuma fam miliyan 5 na tsarabe-tsarabe.
Sanarwar ta Gunners ta zo ne bayan da dan wasan mai shekaru 24 ya fitar da wata budaddiyar wasika ga magoya bayan West Ham yana mai cewa matakin da ya dauka na barin kungiyar ba abu bane mai sauki.
- Xi Ya Nanata Bukatar Samun Ci Gaba Mai Inganci A Fannin Tsaron Intanet Da Aikin Sadarwa
- Manoman Tumatur 70,000 Na Bukatar Tallafin Gwamnatin Kano – Yadakwari
Rice ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar da Arsenal a yarjejeniyar da ke da zabin karin shekara.
Na dubi Arsenal a cikin shekaru biyun da suka gabata da kuma yanayin da suka shiga,” in ji shi.
Ina matukar sha’awar salon wasan da Mikel Arteta yake aiwatarwa.
Rice Shi ne babban dan wasa na uku da Arsenal ta saya a bana, yayin da ta neman tunkarar kakar badi inda ta samu damar buga Champions League.
Zuwansa ya biyo bayan daukar dan wasan kasar Jamus Kai Havertz daga Chelsea kan kudi fam miliyan 65 da kuma dan wasan baya na Netherlands Jurrien Timber daga Ajax kan kudin da zai kai fam miliyan 38.5.
Dan wasa ne da ke da kwarewa sosai, wanda ya taka rawar gani a gasar Premier da kuma Ingila tsawon shekaru da dama in ji kocin Arsenal Mikel Arteta.
Declan yana da kwarewa sosai a gasar Premier yana da shekaru 24 kacal ya zama kyaftin din kungiyar West Ham inda ya taimaka mata lashe kofin Turai.
Arsenal ta yi nasara ne da tayin ta na uku kan Rice, bayan da aka yi watsi da tayi biyu a baya wadanda suka yi kasa da farashin da West Ham ta nema.
Zakarun gasar Premier Manchester City ta janye daga yunkurin siyan dan wasan bayan anyi watsi da tayin fan miliyan 90 da tayi.
Farashin farko na Rice yayi daidai da fam miliyan 100 da City ta biya Aston Villa kan Jack Grealish a 2021.