Arsenal ta fara shirin tsawaita kwantiragin Bukayo Saka da William Saliba da karin shekara daya, in ji ESPN.
Sai dai kungiyar ta Firimiya tana tattaunawa kan yarjejeniyar kara wa ‘yan wasan dogon zango a kungiyar.
Dukkansu, Saka da Saliba sun shiga watanni shida na karshe na kwantiraginsu. Amma kungiyar ta tsawaita wa’adin ci gaba da zamansu a kungiyar har zuwa 2024.
Kungiyar mai jan ragamar gasar Firimiya a yanzun suna da kwarin gwiwar tabbatar da tsayawan ‘yan wasan a kungiyar har zuwa shekaru da yawa masu zuwa.
Ana kyautata zaton karawa Saka albashi mai kwari har zuwa kusan £ 200,000 a duk mako.