Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal FC ta buga canjaras Da abokiuar karawarta Fulham a ranar Asabar.
Wasan shine wasan sati na uku na wannan sabuwar kakar wasa da ake ciki.
- Arsenal Ta Doke Man City Yayin Da Ta Lashe Kofin Community Shield
- Na Yi Mamakin Rashin Nasara A Hannun Arsenal -Xavi
Fulham ce ta fara jefa kwallo a mintin farko da fara wasan ta hannun Andre Peres kafin Saka ya farke kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Eddie Nketiah ya kara jefawa Arsenal kwallo ta biyu kafin dan wasan Fulham Palninha ya dirar da wasan ana gab da tashi.