Shugabar Kotun Daukaka Kara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta ba da umarnin a mayar da duk wata daukaka kara da ta taso daga kararrakin zabe a fadin Nijeriya zuwa kotun Abuja da Legas.
Umurnin ya shafi zabukan gwamnoni, ‘yan majalisu na tarayya da na Jihohi, wanda aka gudanar tsakanin Fabrairu zuwa Maris 2023.
- Tsokaci A Kan Yadda Wasu Mata Ke Baje Kolin Hira A Cikin Motocin Haya
- Sin Ta Kai Daukin Gaggawa Ga Falasdinawa
A farko, ya kamata a saurari kararrakin ne a kotunan daukaka kararrakin zabe na jihohi daban-daban guda 20 da ke fadin kasar amma yanzun Kotun Abuja da Legas ne kadai za su saurari kararrakin.
An bayar da wannan umarni ne biyo bayan zarge-zarge da kararrakin da ake yi wa alkalan kotunan jihohin.
Wasu jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu sun yi zargin cewa, gwamnonin jihar sun saye alkalan kotunan jihar.
Majiyoyi a kotun daukaka kara sun ce, sashin Abuja zai saurari kararraki daga jihohin arewa 19 yayin da za a saurari kararraki daga jihohin Kudu 17 a Legas.