A ‘yan kwanakin nan batun makudan kudaden da gwamantin tarayya ke narkawa ga sashin tallafin mai kuma man ya ki sauki yadda ake so na matukar ci wa al’ummar Nijeriya tuwo a kwarya, inda wasu ke ganin kwalliya ba ta biyan kudin sabulu domin kuwa har yanzu al’ummar kasar na fama da matsatsi da hauhawar farashin kayan masafuri.
Tun ba yanzu ba dai gwamnatin tarayya ta nuna cewa tana ba da tallafin ne domin samar da saukin rayuwa ga talaka da kuma samar musu da yanayin da za su sayi man fetur a farashi mai sauki ta hanyar ware kudi domin ba da tallafi, sai dai farashin Man karuwa yake kuma hauhawar farashin shi ma haka.
Sai dai wasu alkaluma da gwamnati ke fitarwa sun nuna cewa ana kashe kusan naira biliyan 250 duk wata a matsayin kudin tallafi tun shekarun baya, bisa hakan ne gwamnatin tarayya ta bijiro da batun janye tallafin man a watannin baya kodayake wasu sun soki lamarin a yayin da wasu suka nuna goyon bayansu.
Gwamnatocin baya sun yi irin wannan yunkurin na janye tallafin Mai amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, sai kuma Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta dawo da batun ta hanyar kafa sabuwar dokar man fetur ta Petroleum Industry Act (PIA), wadda ta mayar da kamfanin na kasuwanci zalla maimakon na gwamnati ita kadai.
Ministar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmad ta taba bayyana cewar, muddin suka cire tallafin zai bai wa gwamanti damar amfani da rarar kudin don kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya da kuma samun karin kudin shiga daga bangaren Gas da danyen Mai.
Rikita-rikitar dai ya biyo bayan maida kamfanin Mai ta kasa zuwa hannun ‘yan kasuwa ne, wanda a yanzu haka farashin Mai ya zama daban-daban a shiyyoyin kasar nan.
Sannan, bincikenmu ya nunar da cewa masu gidajen mai daban-daban suna sayar da mai kan farashin da ransu ke so.
Tuni dai gwamantin ta fara janye janye tallafin mai sannu a hankali. Ana dai fargabar cewa, idan gwamnati ta samu nasarar janye tallafin gaba daya farashin mai zai iya kaiwa N300 a Lita daya.
A watannin baya Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya kuma Gwmanan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya ce tattalin arzikin Nijeriya “na tsaye cak”, yana mai cewa idan za a cire tallafin dole ne talakawa su amfana ba wasu ‘yan tsiraru ba.
Ya kara da cewa jihohi takwas ne kadai suke amfana da tallafin kai-tsaye, yana mai nuna damuwa kan cin hanci da rashawa da ya dabaibaye sashen mai da iskar gas a kasar. Kan wannan batun ne muka zanta da masu ruwa da tsaki domin jin halin da ake ciki.
A zantawarsa da LEADERSHIP Hausa, malami a sashin tattalin arziki na Jami’ar Jihar Bauchi, Dakta Yahaya Yakubu ya yi gargadi kan janye tallafin mai, saboda za a samu ninkuwar farashin kayan masarufi a maimakon saukinsu.
Ya ce, kafin gwamnati ta cire tallafin kamata ya yi ta fara tunanin samar da Matatun Mai domin sarrafa man a cikin gida Nijeriya.
Daktan ya ce, ba da tallafin na alamta kasashe ne da suke tasowa sakamakon kasancewarsu a yanayi na karancin samun kudaden shiga masu yawa ko kasancewa a tsaka-tsakiya, wanda Nijeriya ma tana wannan sahun ne a halin yanzu.
A cewarsa: “Duk lokacin da ake son tattalin arziki ya ci gaba, akwai bukatar samar da yanayin da mutane za su samu karfin da za su iya sayen kayayyakin da ake samar musu. Idan suna sayen kayan za a samu kudin shiga, daukan ma’aikata da sauran ci gaba wanda hakan zai janyo kudaden shigar kasa su kara habaka.
“A bisa haka ne kasashe masu tasowa ke ba da tallafi domin jama’an su samu damar sayen kayayya har komai habaka.”
Malamin ya ce, bayan duba dalilin ba da tallafin, wanda hakan na da matukar muhimmanci a yanayi da halin da Nijeriya ke ciki, sai ya nusar da cewa, batun tallafin mai da gwamnatin tarayya ke zubawa ga sashin abu ne wanda ya kamata domin kuwa muddin aka cire tallafin halin da ake ciki na tsanani zai fi yadda ake ciki a yanzu.
“Mu duba ma meye ya kawo maganar tallafin da ake badawa. Tallafi a bangaren mai, Nijeriya na da mai da da take samarwa, amma matsalarmu shi ne tun farko ba mu da tsarin sarrafa mai din na yadda za mu tace shi asalin man da muke da shi a kasar nan.
“Sai Nijeriya ta kwashi man ta kai waje a sake sayen taceccensa a shigo da shi. Wajen sayo shi din daga kasashen waje akwai farashin da muke sayen shi.
Idan aka sayo yadda yake zuwa mana nan yana zuwa ne da tsada, halin da ake ciki a kasarmu (mai tasowa) da karfin tattalin arzikin jama’a ba za a iya saya ba; in kuma an ce wa jama’a su saya a haka da kansu zai rage karfin tattalin arzikinsu sosai, don haka gwamnati tana dan sanya tallafi don Mai din ya kai matakin da masu kananan karfi za su iya saya.
“Shi wannan tallafin da gwamnati ke sanyawa shi ne ake maganar a cire. Matsalar shi ne idan har gwamnati ta cire tallafin mai akwai illolin da za su karu, domin idan ka cire tallafin, na daya abu ne wanda ya shafi shi kansa makamashi da hidimar zirga-zirga da sauran abubuwan da suke jibge, don haka za a samu tashin hauhawar farashin abubuwa fiye da halin da ake ciki.
“Gaskiya duk da hauhawar farashin a halin yanzu cire tallafin mai barazana ne sosai, saboda hauhawar tashin abubuwa da ake fuskanta akwai dalilai da dama da suka sabbaba shi.
Wasu matsalolin daga kasashen waje ne wasu kuma daga nan ne, kamar misali yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine shi ma ya janyo matsala saboda wasu abubuwan da ake sayowa daga kasashen Afrika ana sayo su ne a wadannan kasashen biyu shi ya sa wasu abubuwan suka tashi.
“Yanzu idan aka zo aka ce duk da halin da muke ciki a yanzu za a cire tallafin nan lallai matsalolin tashin kayayyakin masarufi ninkuwa za su yi. Ba cire tallafin mai ne ya janyo matsalolin tashin kayayyaki ba, wasu matsalolin ne daban.”
Dakta Yahaya Yakubu ya kara da cewa babbar matsalar da ke akwai a Nijeriya ana duba illar abu ne nan take ba tare da nazarin illar da zai yi a nan gaba ba,
“Ya kamata duk wani tsarin da za a kawo a duba illar da zai yi nan gaba, ba kawai a duba illar da zai yi yanzu-yanzu ba. Sannan kuma duk wani abun da za a yi, idan yau ne to mu sani amfaninsa zai yiyu ya fi ma na yanzu a nan gaba.”
“Mutane suna cewa tallafin mai din nan kawai ya shafi masu ababen hawa ne, a’a ya shafi harkokin rayuwa da dama.
Domin kusan komai da mai abun hawa da marar abun hawa ke amfani da su na kayayyaki sai an yi jigilarsu, don haka da zarar mai na Fetur ko Gas ya yi tsada dole abubuwa su yi tsada.
Idan abu ya faru a wani sashi, zai iya ninkuwa zuwa wani fannin, balle muhimmin sashi na bangaren mai wanda ya shafi harkokin sufuri da zirga-zirga.
Cire tallafin mai din nan ba zallar masu ababen hawa ne za su sha wahalarsa ba, har talakawa za su dandana. Wannan dalilin ne ya sanya kasashe masu tasowa ke ba da tallafin nan domin rage kaifin tsadar man.
“Rashin ba da tallafi ya shafi kasashe ne da suka ci gaba.
Hatta China akwai tallafi domin ita kanta har yanzu tana tasowa ne, Malaysia akwai tallafi domin kasa ce mai tasowa duk da wadannan kasashen suna ci gaba, ba da tallafin shi ne zai kara wa jama’a karfin iya saye da sayarwa har tattalin arzikin ya habaka.
Ko kasashen da suka ci gaba haka suka yi, ai a baya da can suna ba da tallafin kafin su kai matsayin da suke a yanzu da tattalin arzikinsu ya habaka ya girma sai a ce an cire tallafi.”
Masanin ya ce, inda matsalar take a kasar nan ba wai bada tallafin ba ne, cin hanci da rashawa ne ya mamaye harkokin tallafin da har jama’a ba su ganin alfanun narka tallafin mai da gwamnati ke yi.
Ya kara da cewa, akwai matsalar karfin iya tafiyar da tsarin da aka tsara da kumayaki da matsalar rashin da’a da ake fuskanta a ma’aikatu da tabbatar da hukunta wadanda aka kama da laifi, inda ya nuna cewa duk wadannan abubuwan suna shafan tattalin arziki.
“Yanzu misali Malaysia, ina yawan bada misali da Malaysia domin masaniya a kai, suna bada tallafi kamar yadda na fada, tallafin da suke bayarwa ai bai samun matsala domin suna da tsare-tsaren da suke tabbatar da ana bin tsarin da aka samar da yaki da matsalar rashin da’a da rashawa, dokokinsu na aiki, kuma duk wanda aka kama da rashawa za a hukunta shi yadda ya kamata, don haka tallafin da gwamnatin ke badawa yana amfani a inda ya kamata jama’a su na amfana talakawa na morewa.
“Amma idan aka ce akwai cin hanci da rashawa a kasa mutum daya zai yi awun gaba da biliyoyi koda akwai tallafin ka san ba zai kai zuwa ga talakawa ba. Abu na biyu kuma shine, ka ga wannan gwamnatin da ta zo akwai alkawuran da suka yi na cewa za su gina matatar Mai, to har yanzu wadanda ake da su ma ba a gyara ba balle samar da sabbi, don haka gwamnatocinmu ba ma wannan kawai ba har na baya basu da harsashen cewa nan gaba shekara 40 zuwa 50 ina muka dosa.
Ya kamata ne a ce kasar nan tana da tsari na tattalin arziki a ce daga nan zuwa shekara kaza ga abunda ake so na cimma, kafin Malaysia ta kai inda take yanzu sai da ta yi hakan.”
Dakta Yahaya ya nuna cewa abun kunya ne ga Nijeriya a ce har yanzu babu Matatun tashe Mai masu inganci da za su iya saffara albarkatun Mai a cikin Nijeriya har sai an fita da su waje, ya nemi gwamnatocin da su farka, “Yanzu a ce muna da arzikin mai a kasar nan amma ba mu da wuraren tacewa da sarrafa Mai sai mun kai kasashen waje lallai akwai matsala, kuma gwamnatocin ba su tunanin yin hakan.
Babu wani tsarin samar da matatar Mai, da akwai tunanin samar da Matatun Mai duk wadannan matsalolin tsadar Mai din zai zama tarihi balle ma a yi maganar tallafi.”
Ya ce, muddin in gyaran ake nema to fa dole ne a samar da tsari na nemo matatun Mai da kuma hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen tabbatar da yaki da rashawa da cin hanci, yana mai cewa hatta nacewa da aka yi wajen sayo Mai din daga kasashen waje rashawa ne kawai makeale da wasu ke cin gajiyar shi.
Shi kuma wani fitaccen manazarcin lamuran yau da kullum a Nijeriya, AMB Nazeeb Sulayman Ibraheem ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa,
“Tallafin Mai na nufin cikin kudin da dan kasa ke sayen litar Mai, gwamnati za ta rage masa wani kaso daga ciki don rage masa radadin tsadar Man. Misali, dan kasa zai sayi litar Mai a N300.
Maimakon N300 da zai biya, sai gwamnati tace ya biya N200 kawai. Ita kuma Gwamnati ta biya masa N100 daga ciki. Ka ga dan kasa ya samu sauki.”
Ya kuma zayyano wasu da alfanun tallafin ga rayuwar talakawa da cewa, ta na habaka yawaitar kayayyakin saye da sayarwa a kasuwanninmu, haka zalika tallafin na rage azabar da masana’antu ke sha wajen kerawa ko wadata kasuwanni da kayayyakin sayarwa.
“Rage tsadar kudin kkera ababen bukatar ‘yan kasuwa da kwastomomi, da fiddo su kasuwanni don masu bukata. Tallafin Rage kere-kere ko yawaitar abubuwan bukatu iri dabam-dabam da za su bada damar kananan kamfanoni da daidaikun masu sana’a marasa karfi su fito da tasu hajar don a dama dasu.
Wannan zai bada dama ga masu karamin karfi su samu zabin sayen abinda suke so daidai karfinsu tunda ga ababen saye barjak.”
Idan za mu iya tunawa, cikin shekaru biyu kacal (2019-2020) ne Nijeriya ta ajiye Dala Miliyan 7 (Naira Trillion 30) da ta ribato na rarar Mai.
Zuwa wannan shekara da muke ciki, ana sa ran ribar za ta wuce haka.
Wannan na nufin Nijeriya ta kashe sama da $30 Billion kan tallafin Mai a shekaru 16 ko fiye da haka. A shekarar 2018, Nijeriya ta kashe Naira Billion 722 ($2.4 Billion) a kasuwar canjin kudin duniya kan $1 = 306 Naira), amma ta kashe $1.5 Billion kan harkar kiwon lafiya.
Mu sani, koma-bayan harkokin kiwon lafiya a Nijeriya ba zai rasa nasaba da yawan kudaden tallafin Mai da Nijeriya ke kashewa duk shekara ba don talaka ya wala daga yawan karin kudin Mai. AMB Nazeeb Sulayman Ibraheem ya kara da cewa, “A ta bangaren tsaro kuma, dalili na farko da ya sa harkar tsaro ta-ki-ci, taki-cinyewa shi ne batagari irinsu kungiyar Boko Haram, Afenifere, IPOB, ‘Yan Iskan Neja Delta, ‘Yan Fashi da Makami da masu garkuwa da mutane da barayin cikin gida duk sun yi amannar wasu tsiraru ne daga cikin kasa ke wawashe dukiya da kasa ta tara a Nijeriya suna ci da abokansu, dangi, ‘ya’ya da jikoki.
Bakin cikin shugabanni sun yi watsi da matsalar ‘yan kasa, yasa batagari suka ja-daga suna wasusar nasu kason ko ana so, ko ba a so.
“Na biyu, ‘ya’yan talakawa na bore da kone-kone da fashe-fashe don takaicin rufe makarantunsu a ko’ina a fadin kasa da ganin ‘ya’yan shugabanni dana abokansu attajirai na makarantu a kasashen ketare suna walwala da kudin talaka.’ Ya’yan talaka na daukar fansa don a fasa kowa ya rasa.
“Na uku, malaman jami’o’i basu jin kira don sun fahimci hakkokinsu sai sun yi bore a biya musu tunda ga kudin a aljihun tsirarun ma’aikatan gwamnati, ‘yan siyasa da ‘yan bangar gwamnati da barayi.
Na hudu, babu adalci a bangaren rabe-raben ababen more rayuwa daga jiha zuwa jiha. Shi yasa duk kasa ke neman mafita ta wani sabon canji. Wannan na tunzura al’uma ta dauki shari’a a hannunta.”