• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Asalin Abin Da Ya Sa Wata Mata Kashe Mijinta A Bauchi

by Khalid Idris Doya
2 years ago
Bauchi

Idan za ku iya tunawa dai a ranar 5 ga watan Yuli ne wata mata mai suna Maimunatu Sulaiman da ke zama a unguwar Kofar Dumi cikin kwaryar Bauchi ta kashe mijinta Aliyu Mohammad sakamakon rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu.

Bayanai da ke fitowa daga bakunan mutanen yankin unguwar na cewa an samu rashin jituwar a tsakanin miji da matar ne sakamakon yunkurin da Aliyu mijin ya yi na kara aure.

  • Daminar Bana: Sarkin Bauchi Ya Jagoranci Addu’ar Rokon Ruwa

Kazalika, an labarto cewar matar ta daddaba wa mijin nata wuka ne a kirjinsa da hakan ya janyo sanadin mutuwarsa.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 5 ga watan Yulin 2023 a gidan ma’auratan da ke wannan adireshin na unguwar Kofar Dumi.
Domin jin yadda ainihin lamarin ya kasance, LEADERSHIP Hausa ta zanta da daya daga cikin ‘yar uwar mamacin inda ta fayyace zare da abawa.

Ta shaida cewar, akwai maganar mijin zai kara aure amma ya bijiro da maganar ne kawai domin rashin jin dadin zama da matar tasa.

LABARAI MASU NASABA

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

Sannan, ta ce, matar Maimunatu ta na da wasu kawaye da suka janyo mata lalacewar dabi’arta duk da cewa sun yi aure na soyayya da mijinta.

“Shi dai dan uwanmu ne, amma da yake kuma gidanmu na kusa da su, kusan kullum yana shigowa gidanmu sau tarin lokaci ya kan yi korafi a kanta kan wasu dabi’unta da bai gamsu da su ba, hakan kuma yana yawan janyo musu yin fada a tsakani.

“Sannan ita din tana shaye-shaye, domin a ranar da aka yi kisan ma an duba dakinta an ga nau’ikan kayan maye wasu ma har wari suke yi,” a cewar ‘yar uwar mamacin da ta nemi a sakaya sunanta saboda wasu dalilai.
Ta ci gaba da bayani cewa, “Abin da aka iya ganowa shi ne, ta sanya masa maganin sanya barci ne a zobo ta yadda koda za ta caka masa wukar ma ba zai iya komai ba; yadda ta caccaka masa wukar a wajen ko motsawa bai yi ba.

“Lokacin da wansa ya shiga dakin sai ya kira babansa cikin firgici ya ce Baffa ka zo an kashe Ali domin ya ga abin da ke faruwa.
Sai shi baban nasa ya zare wukar daga jikinsa.

‘Lokacin da ta cakka masa wukar, ita ma ta dan yanka kanta, kawuna ne ma ya yi mata dinki.

Da farko kowa ya dauka barayi ne suka shigo suka kashe shi suka kuma jikkata ita matar, dama haka ta so yi domin bayan da ta kashe shi ta yanki kanta sai ta kwanta a kan gawarsa domin jini ya bata mata jiki sai ta yi kamar ta suma.

“Hakan ya sanya jama’a suka dauka ita ma barayi ne suka jikkata su duka. Sai aka dauke ta zuwa asibiti.
“Daga baya da aka gane ba barayi ba ne sai labarin ya canza kuma. Daman ta taba masa irin haka.

Ana saura kwana biyu ma ta kashe shi ta dauki dankwali ta shake masa wuya har wuyan ya kumbura.

“Da ya je gidan Dadarsa sai take tambayarsa meke faruwa sai ya gaya Mata abubuwan da suke faruwa sannan ye ce maza shi kam zai rabu da ita saboda ta na yunkurin kasheshi.”

‘Yar uwan ta shi ta bayyana cewar marigayi Aliyu na sana’ar sanya tayels ne. Ta kara da cewa, akwai zargin da ake yi wa matar tasa na cewa tana mu’amala da wasu muggan kawaye da abokai da suke hure mata kunne, “Ta na da wasu kawaye da take kawowa su barnata gidan.

Sannan in ta je makaranta ba ta dawowa da wuri hakan ya fara sanya zargi a tsakaninsu.
“Tana da aurensa amma ta na da wasu samarin a waje. Abin da zai baka mamaki auren soyayya suka yi amma daga baya ta samu wasu kawaye da abokai gurbatattu suka daurata a mummunar hanya.

“Tana sonsa sosai shi ma yana sonta da farko, amma daga baya da ta samu masu hure mata kunne shi kenan ta baci. Akwai wani da ya mata alkawarin zai aure ta muddin ta rabu da mijinta mai rasuwa.
“Babanta Birkila ne a Gombe ya ke, da yake ya ga kyawun dabi’un marigayin sai ya hada sa aure da ‘yarsa a she ita ce ajalinsa.
“Ya sha kokarin rabuwa da ita amma sai ya ce in ya sake ta bai da kudin da zai kara aure.”

Ta kuma tabbatar da shi marigayin da kansa ya fada kafin ta kashe shi cewar matar tasa tana dauke da juna biyu na wata biyu amma ta zubar da cikin.

Ta misalta marigayin a matsayin mutum na kwarai wanda bai shiga sabgogin kowa sai hakan ya zama dole balle har ya yi fada.
Sai dai a bangaren rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi kuwa, sun ce kawo yanzu sun cafke ita Maimunatu bisa zargin kisan kai.
A sanarwar da mai rikon kakakin ‘yansanda Jihar Bauchi, ASP Aminu Gimba Ahmed ya fitar a ranar Juma’a na cewa, “A ranar 5 ga watan Yulin 2023 jami’an caji ofis din ‘yansanda da ke Township, Bauchi sun kama wata Maimunatu Sulaiman bisa zarginta da aikata kisan kai.

“Lokacin da jami’an suka samu rahoton faruwar lamarin, sun garzaya zuwa inda lamarin ya faru tare da daukar wanda tsautsayin ya rutsa da shi da ita kanta wacce ake zargi zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital (ATBUTH), Bauchi domin kokarin nema musu kulawar Likitoci.”

“Amma Likitoci sun tabbatar mutuwar mijin sakamakon raunuka da ya samu a kirjinsa, yayin da ita kuma wacce ake zargin ta samu wasu ‘yan raunuka kadan a cikinta.”
Binciken ‘yansanda na farko-farko na nuni da cewa wacce ake zargin Maimuna Suleiman ta soki mijinta Aliyu ne a kirjinsa sakamakon rashin jituwar da ta barke a tsakaninsu a gidansu na aure.

A lokacin binciken wacce ake zargin ta amsa laifinta da kanta a cewar sanarwar ta ‘yansanda.

Kan hakan, kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi CP Auwal Musa Mohammad, ya umarci a tura lamarin zuwa sashen kula da manyan laifuka (SCID) domin zurfafa binciken da gano musabbabin faruwar lamarin.

Ya ce za a gurfanar da wacce ake zargin da za a aka kammala gudanar da binciken ‘yansanda.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa
Kotu Da Ɗansanda

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

November 8, 2025
An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi
Kotu Da Ɗansanda

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

November 8, 2025
Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi
Kotu Da Ɗansanda

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

October 4, 2025
Next Post
Gini Ya Yi Ajalin Yara 2 Legas

Gini Ya Yi Ajalin Yara 2 Legas

LABARAI MASU NASABA

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.