Bukuru, hedikwatar karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato, ta fada cikin ruɗani a ranar Litinin da yamma, yayin da wasu ‘yan bindiga suka ƙona motoci 10 tare da lalata gine-gine.
Rikicin dai ya samo asali ne bayan wata arangama da ‘yan barandan suka yi da jami’an tsaro a kasuwar Kugiya da aka rushe. Jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yansanda da jami’an tsaron farin kaya na NCSDC, suna aiwatar da dokar da gwamna jihar Caleb Mutfwang ya sanyawa hannu da nufin shawo kan gine-ginen da ba akan ka’ida ba da kuma karya dokokin hanya.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Ceto Mutane A Katsina Da Filato
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 40, Sun Kone Gidaje Da Dama A Filato
Wani shaidar gani da ido Garba Tanko ya rawaito cewa ƴan ta’addan ɗauke da sanduna da kulake, sun bijirewa jami’an tsaro ta hanyar tayar da zaune tsaye, wanda ya yi sanadiyar kona motoci da shaguna.
Har sai dai da ta kai cewa akwai buƙatar jami’an tsaro su shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo ya ci tura.
Faruwar wannan hatsaniya ta ƙara jaddada ƙalubalen da hukumomi ke fuskanta wajen aiwatar da ka’idojin tsara birane da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin.