Ƙungiyar ASUU reshen Jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU) ta dakatar da yajin aikin da ta fara kusan makonni biyu da suka wuce. A ranar 29 ga Nuwamba, ASUU ta ayyana yajin aiki ne domin neman biyan buƙatunta na rashin tsarin fansho da alawus na mutuwa ga ma’aikatan SAZU da kuma rashin biyan haƙƙoƙin kuɗi na aikin koyarwa da alawus ɗin aiki bayan an tashi.
Shugaban ASUU na jami’ar, Comrade Auwal Nuhu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Litinin. Ya ce an yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne a taron gaggawa da aka yi a ranar 14 ga Disamba, 2024, bayan tattaunawa da ɓangaren Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi.
- Nakasa A Mahangar Karin Magana: Guzurin Ranar Nakasassu Ta Duniya
- Da Ɗumi-dumi: Sakataren Gwamnatin Bauchi Ya Yi Murabus
Comrade Nuhu ya bayyana cewa an sanya hannu kan yarjejeniya (MoU) tare da gwamnatin Jihar Bauchi domin magance matsalolin da suka haifar da yajin aikin. Ya ce, wannan yana nuna jajircewar gwamnati wajen inganta ilimi a Jihar Bauchi, kuma an yanke shawarar dakatar da yajin aikin nan take.