Rudani ya auku a jihar Anambra a yayin zanga-zangar goyon bayan kungiyar malaman Jami’oin kasar nan ASSU da kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta kira.Â
Kungiyoyin da suka suka hade da NLC a jihar sun bi umarnin NLC na fitowa zanga-zangar, sai dai, kungiyar ta ASSU ta nuna rashin dadinta kan yadda aka shirya zanga-zangar, ganin cewa, zanga-zangar ba ta wuce ta mituna 20 ba kacal.
- Da Dumi-Dumi: Sanatoci Sun Lashi Takobin Tsige Buhari Saboda Matsalar TsaroÂ
- Shin Zargin Kasar Sin Ya Fi Yaki Da Ta’Addanci Muhimmanci?
An ruwaito wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar ta ASSU sun zargi kungiyar ta NLC kan yadda aka gudanar da zanga-zangar inda suka sanar da cewa, an tsara za a yi zanga-zangar ne a kan babban titin Enugu zuwa Onitsha yadda za ta yi armashi amma aka samu akasin hakan.
Daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar ASUU ya bayyana cewa, ta yaya za a gudanar da zanga-zangar a cikin mintuna 20 kacal.
Sai dai, shugabar kungiyar NLC reshen jihar, Chinwe Orizu, a jawabinsa a gurin zanga-zangar ta sanar da cewa, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi duba kan bude jami’oin ga ‘ya’yan ASSU da kuma daliban jami’oin don su koma su ci gaba dakaratunsu.
Ta kuma yi kira ga ASSU da ta daina dora lafin a kan gwamnatin tarayya, inda ta danganta hakan da cewa na janyo rudani wajen gudanar da zanga-zangar.
An dai jibge jami’an tsaro a dandalin Dakta Alex Ekwueme, inda ake gudanar da zanga-zangar inda masu zanga-zangar suka yi tattaki daga dandalin zuwa Aroma, inda suka datse babbar hanyar Enugu zuwa Onitsha har zuwa tsawon mintuna biyar hakan ya janyo cunkoson ababen hawa.