Wani matashi mai shekaru 27 mai suna Yayu Musa, ya shiga hannun rundunar sa-kai bayan da ya hallaka surukarsa, Atayi Abdul, a garin Olla, ƙaramar hukumar Omala, jihar Kogi.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar Juma’a. Wanda ake zargin ya yaudari surukarsa da zargin cewa wasu na girbin amfanin gonarta, lamarin da ya sa ta bi shi zuwa gona, inda ya cukume ta har ya kashe ta.
- Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi
- Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Gidan Sanata Natasha A Kogi
Bidiyon da rundunar sa-kai ta ɗauka ya nuna yadda aka sami gawar matar da raunuka da dama a jikinta, alamar cewa an sare ta bayan an kashe ta.
An kama wanda ake zargin a wani gari dake makwabtaka da su bayan rundunar sa-kai ta ƙaddamar da farautarsa. A cikin bidiyon da aka ɗauka, Yayu Musa ya amsa cewa ya aikata kisan saboda fushin da ya ji game da yunƙurin surukarsa na ba wani namiji matarsa, Umi Idris, domin rashin samun ciki.
Ya bayyana cewa ya kashe surukarsa ne saboda ta dinga cewa bai cancanci ya riƙe matarsa ba saboda matsalarta ta haihuwa. Ya ce ya sayar da baburinsa da kashe dukiyarsa wajen neman magani, amma surukarsa ta nace tana neman bayar da ‘yarta ga wani.
Rundunar Ƴansandan jihar ba ta fitar da bayani kai tsaye ba, amma wani babban jami’i da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da kama wanda ake zargi, tare da ce wa an tafi da shi zuwa Lokoja domin cigaba da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp