Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci dan takarar shugaban kasa a jamiyyar PDP Atiku Abubakar da ya bayyana wa ‘yan Nijeriya halin da lafiyasa ke a ciki da kuma zargin da ake masa na karkatar da dukiyar al’umma.
Rahotanni sun bayyana cewa, an fitar da Wazirin na Adamawa zuwa kasar Birtaniya domin a duba lafiyar sa, amma hadimansa, sun hakikance cewa, Atiku ya je kasar ce bisa gayyatar gwamnatin ta Birtaniya
Amma a cikin sanarwar da daraktan kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC Bayo Onanuga ya fitar ya tabbatar da cewa, Atiku bai da cikakkiyar koshin lafiya.
“muna da ingantattun bayanai cewa, Atiku bai da koshin lafiya, ya tafi kasar Birtaniya ne domin duba lafiyarsa, amma wakilansa sun ce, yaje kasar Birtaniya ne bisa gayyatar wasu jami’an gwamnatin kasar kamar yadda suka gayyaci Tinubu da Obi a baya” inji Bayo.
Sanarwar ta kara da cewa, ya kamata Atiku ya dakatar da yin takararsa, ganin cewa zai sake shan kasa a lokacin zaben, musamman biyo bayan fitar da faifan muryar da ya yi bayani dalla-dalla na hannunsa akan cin hanci da rashawa.