Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi shirin shugaban kasa, Bola Tinubu, na rabawa magidanta naira 8,000 cikin wata shida da yunkuri karkatar da kudaden gwamnati.
Atiku ya yi wannan zargin ne cikin sanrawar da babban mai taimaka masa kan sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar.
- Yadda Fintiri Da Atiku Suka Gudanar Da Bikin Sallah A Adamawa
- Atiku Ya Yi Martani Kan Korar Karar Da PDP Ta Shigar A Kan Shettima
Atikun ya ce, shirin na Tinubu na kashe dala miliyan 800 don rage radadi ga ‘Yan Nijeriya ba shi da wani bambanci da irin wanda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi na tallafin Korona, wanda hakan ya tona aisrin wasu ‘yan siyasa na boye abincin da ya kamata a rabarwa da talakawa.
Atiku ya kara da cewa, shirye-shiryen da Buhari ya kirkiro da su sun kare ne kawai wajen kara mayar da ‘yan Nijeriya talakawa baya kamar yadda rahotannin hukumar kiddiga ta kasa ta fitar.