Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna rashin jin daɗinsa game da yadda aka yi wa ɗan Bola Tinubu, Sheyi Tinubu wata karramawa ta musamman daga wani rukuni da ake kira “Nigerian Cadet Network”.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya ce wannan abin bai dace ba kuma yana zubar da mutuncin tsohuwar al’adar rundunar sojin Nijeriya.
- Ɓarayin Wutar Sola Sun Baƙunci Lahira Yayin Da Suke Tsaka Da Kwancewa
- Yankin Xinjiang Na Kasar Sin Ya Kammala Aikin Shimfida Rami Mafi Tsawo A Duniya
Ya ce irin wannan karramawa ta musamman an ware ta ne kawai ga manyan jami’ai da suka cancanta a hukumance.
Atiku, ya kuma tambayi sahihancin ƙungiyar ta “Nigerian Cadet Network”, inda ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa ƙungiyar ba ta cikin rukunin da sojojin Nijeriya suka sani ko amince da su.
Hakazalika, ya nuna damuwa game da yadda aka yi amfani da makamai a cikin karramawar, musamman a wannan lokaci da Nijeriya ke fama da matsalar yaɗuwar haramtattun makamai.
Saboda haka, Atiku ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma kare mutuncin rundunar sojin Nijeriya.