• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku Ya Ziyarci Buhari Da Sarkin Daura Da Kuma Sarkin Katsina

byLeadership Hausa
1 year ago
Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa ya Kai ziyarar Sallah ga tsohon shugaban ƙasa Muhammad Buhari a gidan sa da ke Daura ta jihar Katsina.

Kamar yadda Wazirin na Adamawa ya bayyana cewa ziyara ce ta gaisuwar Sallah ya kaiwa tsohon shugaban ƙasar da Mai Martaba Sarkin Daura.

  • Amfanin Mangwaro Ga Mata Masu Juna Biyu
  • Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Najeriya Sun Gana A Beijing

Haka kuma ya kai irin wannan ziyara ta ban girma ga mai martaba sarkin Daura, Alhaji Umar Faruƙ Umar domin yin gaisuwa da sada zumunci.

Bayan kammala ziyarar a garin Daura tsohon mataimakin shugaban kasar ya wuce garin Katsina domin yin ta’aziya ga mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman na rashin ɗan Abdallah da ya yi a cikin wannan satin nan.

Atiku Abubakar dai ya ƙara miƙa ta’aziya da jaje ga al’ummar jihar Katsina na kashe-kashen ‘yan bindiga da suka addabi wasu yankunan jihar.

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Kazalika tsohon mataimakin shugaban kasar ya kai irin wannan ziyara gidan marigayi tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita, bisa rasuwar babbar matarsa Hajiya Yalwa Lawal Kaita wanda ta rasu ana cikin hidimomin Sallah.

Daga cikin cikin waɗanda suka rufawa Wazirin Adamawa baya sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da kuma jiga-jigan jam’iyyar PDP irin Dakta Mustapha Inuwa da Sanata Umar Ibrahim Tsauri da Hon. Mustapha Musa Yar’adua da Hon. Salisu Lawal Uli da sauran magoya bayan jam’iyyar PDP a Katsina.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Next Post
Firaministan Kasar Kyrgyzstan: Layin Dogon Da Ya Hada Kasashen Sin Da Kyrgyzstan Da Uzbekistan Zai Taimaka Ga Raya Kyrgyzstan Har Ta Zama Mahadar Jigilar Hajoji

Firaministan Kasar Kyrgyzstan: Layin Dogon Da Ya Hada Kasashen Sin Da Kyrgyzstan Da Uzbekistan Zai Taimaka Ga Raya Kyrgyzstan Har Ta Zama Mahadar Jigilar Hajoji

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version