Ɗan takarar shugabancin kasa a inuwar jam’iyyar PDP ta hamayya, Atiku Abubakar, na shirin kai ziyara birnin Kano a gobe Lahadi domin karbar Sanata Ibrahim Shekarau a jam’iyyarsu.
BBC Hausa ta rawaito cewa, ziyarar ta Atiku da wani makusancinsa ya tabbatarwa BBC na zuwa ne adaidai lokacin da ake dakon jin matsayar Sanata Shekarau da tun a makon da ya gabata ake jita-jitar zai fice daga NNPP.
- Da Dumi-dumi: Atiku Ya Gana Da Wike A Landan
- “Ba Zan Mara Wa Atiku Ko Wani Dan Takara Na Kyale Tinubu Ba” —Buhari
A farkon wannan makon mai ƙarewa tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya nuna alamonin raba gari da jam’iyyar NNPP.
Sanata Shekarau a wata hira da ya yi da BBC ya zargi jagoran jam’iyyar NNPP kuma ɗan takarar shugaban kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da yaudararsu.
Sannan ya shaida cewa suna kan tattauna da tuntubar juna domin sanar da matsayarsu kan ci gaba da zama a NNPP ko akasin haka.
Sai dai majiya mai karfi daga bangaren Atiku ta tabbatarwa da BBC cewa a gobe Lahadi Atiku zai gana da Shekarau a Kano a shirye-shiryen tabbatar da komawarsa PDP.