Atletico Madrid ta amince ta biyan fam miliyan 81.5 don siyan dan wasan gaban Manchester City Julian Alvarez.
Idan har hakan ta faru an yi wannan ciniki, hakan zai sa Alvarez ya zama dan wasa mafi tsada da Man City ta taba sayarwa a tarihinta, inda zai doke abin da Chelsea ta biya na Yuro miliyan 55 wajen daukar Raheem Sterling a shekarar 2022.
- Gwamnatin Kano Ta Sake Sassauta Dokar Hana Fita
- Zanga-zanga: Tinubu Bai Damu Da Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki Ba – PDP
Tun da farko Alvarez ya ce zai jira har sai an kawo karshen gasar Olympics da ake bugawa a kasar Faransa, wanda kasar Argentina ta kai zagayen Quarter Final kafin kasar Faransa mai masaukin baki ta fitar da Argentina a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kocin kungiyar Pep Guardiola ya na sha’awar ci gaba da rike dan wasan mai shekara 24, inda ya ce Alvarez yana cikin ‘yan wasan da yake alfahari da su kafin fara kakar wasa ta bana.
Kamar yadda ta saba Man City ba ta rike duk wani dan wasanta da ya nuna sha’awar barin kungiyar muddin an samu wanda yake nemansa, kamar yadda ta faru da Ilkay Gundogan, Riyad Mahrez da Aymeric Laporte.