Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya naɗa uku daga cikin Kwamishinoni biyar da ya sallama daga muƙamansu a matsayin manyan masu ba shi shawara a ɓangarori daban-daban.
Idan za ku tuna dai mun labarto cewa gwamnan da safiyar ranar Talata ya sallami Kwamishinonin guda biyar da suka haɗa da: Dakta Jamila Mohammed Dahiru – daga ma’aikatar ilimi; Barista Abubakar Abdulhameed Bununu – Tsoron Cikin Gida; Kwamared Usman Danturaki wanda aka kora a matsayin Kwamishinan watsa labarai; Farfesa Simon Madugu Yalams – Ayyukan Gona sai kuma Kwamishina a ma’aikatar harkokin addinai, Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza
- Hatsarin Kwale-kwale: Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya Ta Ceto Jami’an ‘Yansanda 8 Da Wani A Bayelsa
- Adadin Kudin Ajiyar Sin Na Ketare Ya Ragu Zuwa Dala Tiriliyan 3.2024
Sai dai awannin da wannan matakin, gwamnan ya naɗa uku daga cikinsu a matsayin manyan Mashawarta domin su ci gaba da amfani da gogewarsu wajen taimaka wa gwamnatin jihar a ɓangaren gudanar da harkokin mulki.
Sabbin waɗanda gwamnan ya naɗa a matsayin manyan masu ba shi shawara sun ƙunshi, Hon. Abubakar Abdulhameed Bununu – babban mashawarci a ɓangaren haɗa kan jama’a da yankuna; Kwamared Usman Danturaki – mashawarci kan harkokin kwadago da shirin taimakekeniyar Fansho yayin da lima Farfesa Simon Madugu Yalams – Mashawarcin kan fasaha da ilimin koyon sana’ar hannu.
A wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar, Mukhtar Mohammed Gidado ya fitar a daren ranar Talata, ya ce, naɗe-naɗen da suka fara aiki nan take an yi ne da nufin gwamnan na kyautata shugabanci da janyo kowa a jika haɗi da muradun cimma nasarori kan burikan gwamnati mai ci.
Gwamnan ya hori sabbin waɗanda ya naɗan da su yi amfani da gogewarsu da ƙwarewarsu wajen ba da tasu gudunmawar wajen cimma kyawawan ayyukan raya jihar. Kana, ya nemi su yi aiki tsakani da Allah domin kyautata rayuwar al’ummar jihar Bauchi.
Gwamnan ya jaddada aniyarsa na tabbatar da gaskiya da rikon amana hadi da gudanar da mulki na kowa da kowa domin ciyar da jihar zuwa gaba.