Jami’an ilimi kwararru ne a bangaren ilimi wanda aikinsu shi ne da alhakin bunkasawa, aiwatarwa,da kuma tsara manufofin ilimi da tsare tsare.Suna bada gudunmawa wajen tabbatar da cewa kowa yana samun ingantaccen ilimi mai nagarta. Jami’an ilimi sune yin aiki ne a wurare daban- daban da suka hada da hukumomin gwamnati, wuraren ko hukumomin da ba a kafa su saboda su samar da riba da kuma makarantun ilimi. Gudunmuwoyin da jami’an ilimi suke badawa suna da yawa.
Suke da alhakin shirya bincike da kuma nazari domin su gano wuraren da suke da matsalolin da suka shafi ilimi, da kuma samar da hanyoyin da za ayi maganinsu. Hakanan ma jami’an ilimi suna samar da shawarar data kamata da kuma taimako ga Malamai da sauran masu harkar data shafi ilimi domin tabbatar da cewa suna bada nagartaccen ilimi ga dalibai.
- Kidayar Jama’a Da Harkar Ilimi
- Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Kudin Shiga Na Naira Tirililan 34.8 A 2025
Bugu da kari suna kuma taimakawa wajen samar da yadda za a tafiyar da lamari, tsara shi, da yadda za a gabatar horarwa,da rika bibiyar yadda ake aiwatar da duk wani taimakon da ake ba ilimi.Wannan ya hada bayan aikin su Malamai da kuma masana ilimi, jami’an ilimi har ila yau suna mu’amala da Malamai, dalibai da sauran masu ruwa da tsaki ta bangaren ilim.
Suna aiki domin su kulla dankon zumunci da hadin gwiwa domin tabbatar da cewar ana biyan duk bukataun kowa. Hakanan ma su jami’an ilimin suna bada gudunmawa wajen bibiyar yadda ake aiwatar da tsare- tsare da manufofin ilimi kamar yadda ya dace. Suna amfani ne da fasahar zamani da sauran wasu abubuwan da suka zama sheda domin gano wuraren da suke da bukatar da a kawo masu dauki, da daukar matakan da za su samar da canji.Maganar gaskiya jami’an ilimi suna da muhimmanci saboda tabbatar da kowa ya samu ilimi, babu bambanci mai kuma inganci.Ayyukansu na taimakawa wajen yadda ilimi zai iya kasancewa a gaba da kuma tabbatar da cewa dalibai sun samu mizanin ilimin daya dace su samu.Duk hakan na kasancewa ta wajen samar da yadda ya dace a tafiyar da lamari, taimakawa, da jagoranci, jami’an ilimi har ila yau suna samar da yanayi maikyu da yake bunkasa koyon ilimi ga masu koyo da ke koyawa ilimin. Digiri satifiket na shedar Ilimin ya kamata ace jami’in ilimi ya mallaka
Jami’in ilimi mutum ne wanda alhakin kulawa da ilimi ake aiwatar da shi tare da dukkan tsare- tsare ko manufofi suka rataya a wuyansa, ko dai a wata hukuma ko kuma wurin da al’umma suke. Idan mutum na bukatar zama jami’in ilimi akwai bukatar ace ya mallaki takardar shedar ilimi.Ko kuma a kalla yana da digiri na farko a sashen da ya shafi ilimi. Duk da hakan ma ana bukatar da yana da kwarewa ko ya taba aikin koyarwa ko kuma ilimin da yake da alaka da tafiyar da harkar mulki ya kan zama dole hakan. Idan ana maganar dabara kuma jami’in ilimi abin so ne ace ya mallaki ko yana da dabarar iya hulda da al’umma kwarai da gaske, domin kuwa zai rika hulda ne da mutane daban- daban da suka hada da Malamai, dalibai, Iyaye,da sauran masu fada aji ta bangaren ilimi.Akwai bukatar su kasance sun san makamar tafiyar da manufofin ilimi da yadda za a aiwatar da su,da kuma samun mafita daga wasu.Su kasance sun nakalci da sanin yadda za a tafiyar da harkokin ilimi sosai.Ga kuma su iya tafiyar da ayyukan kan lokacin da aka ce masu,kai hara ma da su bunkasa da kuma tsare- tsare da manufofin ilimi.