Jami’an ilimi kwararru ne wadanda suke bada muhimmiyar gudunmawa wajen ci gaban makarantun ilimi,wajen tabbatar da cewar suna bin matakan ilimin da gwamnati ta amince ayi amfani da su.
Ayyukan jami’an ilimi sun sha bamban wannan kuma ya danganta ne da irin nau’in ilimin,amma babban aikinsu shi ne su kasance masu lura da yadda abubuwa suke tafiya tsakanin gwamnati da makarantu.
- Kauyuka Suna Kokarin Neman Cimma Burin Samun Wadata Tare A Kasar Sin
- Duniya Na Fatan Sin Da Amurka Za Su Cika Alkawuransu Cikin Hadin Gwiwa
Suna tabbatar da cewa makarantu suna suna bin dokoki da tsare- tsare wadanda gamwnati ta ce sai an yi amfan da su,inda za su rika bin diddiki na sanin yadda abubuwa suke ta hanyar byin ziyarce- ziyarcen makarantun.Jami’an ilimi sune ke da alhakin tabbatar da cewa makarantu suna da isassun Malamai, kayan koyarwa, da kuma isassun abubuwan da za su taimaka wajen samar da nagartaccen ilimi. Suna aiki ne domin su inganta nagartar ilimi wajen samar da Malamai da kuma dukkan hore- horen da suka dace da kuma taimakon da ake bukata domin a samu bunkasa ilimi ta hanyar samar da Malamai da dukkan hore- horen inganta ilimi da suka kamata ayi masu domin tabbatar da ana samar da ingantaccen ilimi ga dalibai masu neman ilimi. Jami’an ilimi suna yin aiki da jami’an hukumomin makarantu domin su samar da tsare- tsare da ke sanadiyar jin dadin dalibai,da kuma inganta gaba dayan yadda ko inganta yadda koyarwa za ta jawo hankalin dalibai.Jami’an iimi har ila yau sune ke da alhakin nazarin yadda kwazo, fahimta,ko gane abubwan da ake koyawa dalibai suna tafiya kamar yadda ya dace,suna tabbatar da su daliban suna yin abin da ake bukata da ya shafi ilimin su. Suna yin aiki kafada- kafada da Malamai wajen samar da muradan koyarwa masu kyau da za su taimakawa dalibai cimma burinsu na karatu.Hakanan ma jami’an ilimi suna kokarin irin daliban da basu gane abubuwan da aka koya masu ba kamar yadda ake so,ta haka kuma za su taimaka masu da dukkanin abubuwan da suka kamata, da za su taimaka ma su kara kwazon su.Daga karshe jami’an ilimi kwararru ne masu matukar amfani wadanda burinsu bai wuce tabbatar da makarantu suna samar/ bada ilimi mai nagarta ga dalibai.Suna aiki domin tabbatar da makarantu suna aiki da dokoki, tsare- tsare, kula da jin dadin dalibai, da kuma inganta gaba dayan abubuwan da suke bunkasa koyarwa da gane darussan da ake koyawa kamar yadda ya dace.Bugu da kari jami’an ilimi suna aiki tare da Malamai domin su samar da hanyoyin koyarwa ga Malamai wadanda suma kansu hakan zai taimaka masu taimakawa daliban da suke da matsalar gane abubuwan da ake koya masu.
Jami’an ilimi wasu kwararru ne da suke da alhakin lura da yadda ake tafiyar da harkokin ilimi da ganin al’amura na tafiya kamar yadda ya dace su kasance musamman ma a hukuma.Suna ayyuka da suka sha bamban da juna amma duk muradan daya ne kamar a makarantu, Kwalejoji,da kuma Jami’oi, da sauran makarantu inda ake harkar ilimi.Ayyukan jami’an ilimi sun sha bamban wannan kuma ya danganta ne ga irin hukumar da suke yi wa aiki, sai dai abinda aka fi sani sune masu samar da tsare- tsaren ilimi da kuma aiwatar da su gwargwadon yadda su muradan hukumar ko ita makarantar. Suna ma tabbatar da cewa su manhajojin da yadda ake koyawa dalibai hakan ya yi dai dai da irin mizanin da ake son cimmawa kan yadda dokoki suka amince da ayi. Abin na su bai tsaya anan ba domin kuwa har ma suna kafada-kafada da Malamai, jami’an makaranta,da sauran ma’aikatan wurin domin a gano wuraren da ake bukatar a maida hankali na lamarin da ya shafi tafarkin ilimin.Suna samar da horo da ci gaban kwarewa tare da samar da wata kafa ga Malamai, abin bai tsaya kan su ba kadai, domin kuwa har ma da dalibai, wadanda watakila suna da bukatar wani karin haske dangane da abubuwan da ake koya ma su