Yadda jami’in ilimi za iya aiki da Makarantu ko Jami’o’i
Jami’in ilimi yana aiki kafada – kafada da Makarantu da kuma Jami’oi domin tabbatar da ana ba dalibai ilimi mai nagarta. Wannan ya hada da kai ziyara akai- akai ga su Makarantun domin a rika duba wani irin hali su ke dangane da darussan da ake koyarwa da kuma dabarun da za a koya su saboda a tabbatar da ana samun fahimtar wadanda ake koyawa da gane irin kwazon su.Jami’an ilimi suna hadin gwiwa da Malaman makaranta domin su fahimci me ake ciki, ko akwai wuraren da ake bukatar a kara mai da hankali ba domin komai ba sai don saboda a kara samu n fahimta dai dai gwargwado ta abubuwan da ake koya masu.
Bugu da kari sune ke da alhakin duba yadda makarantu suke, su rika sa ana tsaren tsaren da za su bunkasa ilimi, su kuma rika shirya horarwa ga kwararru ta bangaren ilimi.Babban burinsu shi ne a samu hanyar bunkasa ilimi mai nagarta,a kuma bada gudunmawa wajen yadda za a samu gabar wadanda ake koyawa ta yi tasiri ga al’umma baki daya.
Yadda rayuwar jami’in ilimi take kasancewa
Jami’in ilimi shi ne ke da alhakin samarwa da gabatar da tsare tsaren ilimi a cikin Makarantun gwamnati.Matakin ilimin shi yana faraway ne da digiri a lamarin da ya shafi ilimi ko kuma darasin da yake da alaka da shi, sannan kuma shekarun da ya yi yana aiki a bangaren ilimi. Akwai kuma bukatar samun horarwa ko kara ilimi/karatu wanda ake bukata domin samun hawa wani mukami ko, wato kamar na manya, wannan yana nufin kamar, babban jami’in ilimi ko kuma darektan ilimi.Yana kuma da wasu abubuwan da suka kara ma shi kwar jinin samun aikin, ya iya tafiyar da shugabanci,yana da wasu abubuwan da nan da nan z a su taimaka ma shi wajen daukar mataki daukar matakin da ya dace, domin samun damar hawa kan mukamin jami’in ilimi.Sai kuma abubuwan da ake ganin za su iya taimakawa ya zamanto suna da yawa ta wasu bangarorin da suke da alaka da ilimi, kamar yadda za a tsara hanyar koyarwa a ci gaban ta.
Irin albashi da ya kamata a rika ba jami’in ilimi
Aikin jami’in ilimi shi ne ke da alhaki tsarawa, aiwatarwa gudarin tsare- tsaren ilimi da suka kamata a koyar, sai kuma kula da ziyarar domin ko abubuwan da suka dace a koyar ana koyar da hakan, a tsarin makarantu da kuma Hukumomi. A wasu bayanan da aka samu daga yadda ake biyan albashin masu irin mukaman shi ne, albashin jami’in ilimi ya bambanta daga dala 40,000 zuwa 80,000 kowace shekara.Duk da haka albashin yana sauyawa wannan kuma ya danganta ne kan irin matakin ilimi, kwarewa,da kuma wurin da yake.
Bayan albashin ma jami;in ilimi yana amsar kudin inshorar lafiya, shirin ritaya, da kuma yadda za a biya shi hakkinsa idan wani abu ya taso.Gaba daya dai lamarin aikin jami’in ilimi akwai abubuwa masu taimaka ma sa a matsayin shin a jami’in ilimi domin ya samu nasarar tafiyar da rayuwar sa.
Yadda jami’in ilimi zai kasance ya san duk irin ci gaban ilimi da sabbin dabarun da ake ciki
Jami’in ilimi wani mutum ne wanda yake aiki karkashin bangaren ilimi shi ne kuma yake da alhakin tabbatar da cewar ana aiwatar da tsare- tsaren ilim kamar yadda ya kamata.Domin kasancewa cikin sanin irin ci gaban da aka samu kan irin tafarkin ilimi, jami’an ilimi suna halartar tarurruka na karawa juna ilimi, da kuma hororwa lokaci zuwa lokaci, su kan shiga kungiyoyi na wadanda ake kira kwararru, su kuma rika karanta mujallu da suke magana kan ilimi,ko kuma wallafe- wallafe.Suna ma kasancewa cikin lmri na musayar ra’ayi da sauran masana a bangaren, inda za su rika yin musayar ra’ayi ta kafar sadarwa ta zamani da kuma kungiyoyi, haka za su ci gaba da kasancewa domin ci gaban sun a matsayin kwararru.
Saboda kuwa sun sa kan su dole sai sun irin halin da ake ciki kan irin nau’in karatu mai nagarta, jami’an ilimi suna tabbatar da cewa suna bada shawara mafificiya da dukkan abubuwan da suka kamata ga abokan aikin su da kuma dalibai.
Irin matsalolin da jami’an ilimi su kan fuskanta a tafarkin aikinsu
Jami’an ilimi suna fuskantar matsaloli masu yawa wajen gudanar da aikinsu. Daya daga cikin matsalolin ita ce yadda zai rika tafiya daidai da zamani a bangaren ilimi, wato kamar yadda sauyin manufofi ta fasaha ke shafar ilimi lamarin kuma na yin matukara tasiri kan ilimi . Bugu da kari jami’an ilimi har su kan kaucewa bin ka’ida wani lokaci ba domin komai ba sai saboda, su biyawa kowa hakkin sa daga cikin masu ruwa da tsaki da suka hada da dalibai, Iyaye,da kuma jami’an tafiyar da ayyukan makarantu sashen mulki.
Wata matsalar ita ce yadda zai samar da, kuma gabatar da tsare- tsare da manufofi na ilimi, wadanda su kan taimaka wajen ci gaban nasarar dalibai, yayin da har ila yau suna yin kokari na yadda za’ a tabbatar kasafin kudin da aka ware yayi dai dai da bukatun ilimin da ake da su.Gaba daya shi jami’an ilimi suna bada muhimmiyar gudunmawa wajen daukaka ilimi amma aikinsu ya kasance yana da na shi matsalolin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp