Gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal, ta dau alwashim hukunta Aisha Tsafe da aka kama da azabtar da yarinya ‘yar shekara 12 da wuta.
An rahoto cewa, Aisha Tsafe ta kona leda a wuta ne sannan ta daukota ta na diga wa yarinyar a bayanta.
- Kwamitin Majalisar Dattawa Ya Nemi A Karawa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Kudi Kan Kasafin 2024
- Uwargida Ta Lashe Lambar Yabo 23, Ta Zama Jarimar Shekarar 2023 A Karatun Likitanci A Jami’ar Danfodiyo
Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar, Dakta Nafisa Muhammad, ta tabbatar da matakin Gwamnati na hukunta Matar wacce aka ce kishiyar Uwar Yarinyarce, a yayin da ta ziyarci yarinyar mai suna Safiya Tsafe.
Dakta Nafisa Muhammad tayi kira da babar murya kan a hukunta Aisha Tsafe da ta azabtar da diyar kishiyar ta ‘yar Shekaru 12 Safiya.
Jami’in yada labarai na Ma’aikatar mata da Jindadin al’umma, Suleman Isa ne ya bayyana haka a takardar da ya sanyawa hannun ga manema labarai a Gusau.
Tun da farko, mahaifiyar Safiya, Malama Maryam Muhammad, ta roki gwamnatin jihar da kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka wajen bin hakin diyarta, Safiya.
Mahaifiyar Safiya ta gode wa Kwamishiniyar da wasu jami’an kungiyoyi masu zaman kansu da suka nuna damuwa kan abin da ya faru da ‘yarta.