Hukumar da ke kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC), ta ce ba a samu salwantae rai ko guda daya a iftila’in gobara da ya barke a shelkwatar hukumar da ke Abuja a safiyar ranar Juma’ar nan ba.
Daraktan yada labarai na hukumar, Mista Eddy Megwa, a wata sanarwar da ya fitar kan wannan gobarar, ya ce gobarar ta kama ne wajajen karfe 7:30 na safiyar ranar Juma’a kuma ta tsaya ne a iyaka hawa na uku na ginin benen mai hawa shida.
- Sauya Kudi Kokari Ne Na Haramta Amfani Da Naira – Sunusi Ata
- 2023: Kotu Ta Tabbatar Da Uba Sani A Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC A Kaduna
Ya ce, cikin gaggawa da hanzari jami’an ‘yan kwana-kwana reshen birnin tarayya da jami’an kashe gobara na tarayya sun kashe gobarar cikin hanzari.
Megwa ya ce kayan wutar lantarki ne suka janyo gobarar daga sashin tsare-tsare da bincike na hukumar ta NYSC.
“Ba a samu asarar rai ko guda a wannan gobarar ba kuma dukkanin kundaye da muhimman takardun da suka dace an kwashesu aka kiyayesu.
“Kan hakan muna jinjina wa jami’an kashe gobara a bisa hanzarin kawo dauki don kashe gobarar nan.
“Sannan muna godiya wa jami’an tsaro bisa gudunmawar da suka bayar a yayin wannan hatsarin”.