Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a tarihin Nijeriya ba a taba zabe mai karancin tashe-tashen hankula kamar na 2023 ba.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed shi ya bayyana hakan a Birnin Washington a yayin ganawarsa da wasu cibiyoyin siyasa a babban birnin kasar Amurka.
Ministan ya je Washington ne don yin tattaunawa da kafofin watsa labarai na kasa da kasa da cibiyoyin siyasa da sauransu, don samar da mafita ga kalubalen duniya.
Daga cikin wadanda ministan ya tattauna da su kan zaben 2023 da aka kammala sun hada da Cibiyar Hudson, Majalisar Atlantika da Cibiyar Wilson.
Dangane da bayanan da wata gamayyar kungiyoyin farar hula a Nijeriya ta fitar, Mohammed ya ce an samu rahoton mutuwar mutane tsakanin 13 zuwa 28 a zaben da aka kammala, shi ne mafi karanci tun bayan zaben 1964/65.
Mohammed ya ce a shekarar 1964/1965, a kalla mutane 200 ne suka mutu sakamakon rikicin zabe.
Ya ce zaben 1993, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 100, a shekarar 1999 an samu mutuwar mutane 80, zaben 2003 ya yi sanadiyar mutuwar mutane 100, sannan an yi asarar rayuka 300 a zaben 2007.
A cewar ministan, zaben na 2011 ya yi sanadiyar mutuwar mutane 800, zaben 2015 ya yi sanadiyar mutuwar mutane 100, yayin da aka samu asarar rayuka 150 a zaben 2019.
Ministan ya jaddada muhimmacin rayuwa, inda ya bayyana cewa bai kamata dan Nijeriya ya rasa rans aba a lokacin zabe.Ya ce za a iya gudanar da zabe ba tare da rasa rai ba.
Mohammed ya ba da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba kasar za ta kai ga matakin gudanar da zabukan kasa baki daya ba tare da an samu asarar rayuka ba.
Da yake mayar da martani ga kiraye-kirayen da ‘yan adawa suka yi na a soke zaben 2023, bisa zargin tashe-tashen hankula, ministan ya ce hakan babu adalci kuma abu ne wanda bai dace ba.
Ya ce ‘yansanda sun ba da rahoton tashe-tashen hankula da aka samu a ko’ina a kasar, amma ba su kai ga soke zaben ba.
Da yake magana kan rahoton ‘yansandan, ministan ya ce akwai kararraki 489 na laifukan zabe, sannan an kama mutum 781 da za a gurfanar da su a gaban kotu.
A cikin nazarin rahoton da ministan ya yi, ya ce an samu tashin hankali ne na kashi daya tak a sama da rumfunan zabe 300, wanda a cewarsa hakan bai wadatar ba a soke zaben.