• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba A Yabon Dan Kuturu…

byCMG Hausa
2 years ago

Daga ranar 18 zuwa 19 ga wannan wata ne, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kawo ziyara kasar Sin, ziyarar da masana suka ce tana da babbar ma’ana duk da cewa, yanzu dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matsala mafi tsanani, tun bayan da kasashen biyu suka kulla dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu, wanda bai dace da moriyar jama’ar kasashen biyu da ma begen da kasa da kasa ke yi ba.

Sin dai tana kokarin raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Amurka cikin lumana da yadda hakan zai amfanawa duniya baki daya.

  • Sin Na Son Yin Hadin Gwiwa Da Dukkan Bangarori Don Inganta Ci Gaban Da Aka Samu Na Dogon Lokaci Na Hadin Gwiwar Ayyukan Raya Kasa Da Kasa

Kana tana fatan kasar Amurka za ta fahimce ta bisa hakikanin yanayi, da yin kokari tare da kasar Sin din, wajen tabbatar da tushen siyasa na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da daidaita matsaloli yadda ya kamata, da kokarin aiwatar da shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a tsibirin Bali, da sa kaimi ga maido da dangantakarsu bisa turbar da ta dace.

Bangaren Amurka dai ya sha alkawarin mutunta alkaruwan da sassan biyu suka cimma a lokuta da matakai daban-daban don inganta alakar sassan biyu, amma sai a wayi gari Amurka ta sake mayar da hannun agogo baya.

A jawabinsa yayin ganawa da shugabannin Sin yayin ziyararsa a Beijing, Blinken ya bayyana cewa, Amurka na mutunta alkawuran da shugabannin kasashen suka ya yi, kuma Amurka ba ta neman “sabon yakin cacar baka”, ba ta neman sauya tsarin kasar Sin, ba ta neman adawa da kasar Sin ta hanyar karfafa kawance, kana ba ta goyon bayan ‘yancin kai na yankin Taiwan”. Amurka ba ta da niyyar yin rikici da kasar Sin, kuma tana fatan yin mu’amala mai zurfi tsakanin manyan jami’anta da kasar Sin, da kiyaye hanyoyin tattaunawa marasa shinge, da warware bambance-bambancen dake tsakaninsu, da neman tattaunawa, da yin musaya da hadin gwiwa. Sai dai masu iya magana na cewa, ba a yabon dan kuturu sai ya shekara da yatsa. Ma’ana sai mun ga Amurka ta cika wadannan kalamai da ta fada.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Hanya mafi dacewa ta warware batutuwa da suka shafi kasa da kasa, ita ce tattaunawa, maimakon ware kai, da mayar da wasu saniyar ware, da yin komai a bayyane, da damawa da kowa da kowa, tare da ci gaba da shawarwari da yin hadin gwiwa, maimakon yin fito na fito.

Haka kuma, ya dace a rika martaba zabin kasashe na samun bunkasuwa, maimakon fakewa da wani batu na siyasa ko wata manufa da nufin cimma wata moriya ko neman tayar da fitina a sauran kasashe.

Sanin kowa ne cewa, takarar manyan kasashen duniya ba ta wakiltar yanayin da ake ciki, kuma hakan ba zai taba iya magance matsalolin Amurka ko kuma kalubalen da duniya ke fuskanta ba.

Sannan bai dace wani bangare ya yi kokarin siffanta daya bangaren bisa son ransa, sannan ya hana daya bangaren hakkinsa na samun ci gaba ba. Abin jira a gani dai shi ne, ko Amurka za ta cika alkawuranta? Kyawun alkawari dai aka ce cikawa. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Kai Harvertz Ya Koma Arsenal Daga Chelsea

Kai Harvertz Ya Koma Arsenal Daga Chelsea

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version