Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru, ya danganta rahoton da aka wallafa cewa, gwamnatinsa na kashe Naira biliyan 196.9 domin duba lafiyar masu juna biyu a jihar, inda ya ce, rahoton na kanzon kurege kuma an wallafa shi ne, don a bata masa suna.
Badaru ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan ayyuka na musamman, Auwalu Sankara, inda gwamnan ya ce, gwamnatinsa ta ware Naira 600,000,000 a cikin kasafin kudi don duba lafiyar masu juna biyu a jihar, inda Naira 226,740,800 kacal, aka fitar.
- Ba Zan Zauna A Wurin Da Ba Adalci Da Mutunci Ba – Sanata Shekarau
- 2032: Ku Daina Aiko Mana Korafe-Korafen Karya, ICPC Ta Gargadi ‘Yan Siyasa
Ya kara da cewa, gwamnatin ta zabo masu juna biyu guda 20 daga kowace mazabar da ke a jihar guda 287, inda wadanda suka amfana jimmalarsu ta kai 5,740, inda ake ba su Naira 4,000 duk wata.
Ya kuma soki wakilin kafar da ta wallafa rahoton da kuma Editan kafar bisa gazawarsu ta tantance cikakken bayanan da Babban Sakataren Ibrahim Rabakaya, ya gabatar a lokacin taron bita da aka yi a Jihar Kano.