Masarautar Bauchi ta bayyana cewa ba Gwamna Bala Muhammad, ba ne ya dakatar da bikin hawan Daushe na bana ba, kamar yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba. A cewar Masarautar, kwamitin hawan ne da kansa ya rubuta buƙatar a ɗage hawan, tare da neman amincewa daga gwamnatin jihar, wadda kuma ta amsa da zuciya ɗaya.
A cikin wata sanarwa da Magatakardan Masarautar, Alh. Shehu Mudi Muhammad, ya fitar a daren Juma’a, ya jaddada cewa an samu ruɗani sakamakon rahotannin da ke nuna cewa Gwamna ne ya bayar da umarnin soke hawan.
- Hajjin Bana: Dole A Yi Wa Maniyyatan Bauchi Riga-kafin Foliyo – Hukumar Alhazai
- Gwamnatin Bauchi Ta Ɗage Hawan Daushe Na Sallar Bana
Sanarwar ta bayyana cewa wannan batu ba gaskiya ba ne, domin ba gwamnati ce ta nemi a dakatar da hawa ba, illa kawai ta amince da shawarar da kwamitin masarautar ya gabatar.
Masarautar ta bayyana damuwa kan yadda wasu ke ƙoƙarin ɓata sunan Gwamnan a idon jama’a, tare da kira da a dakatar da yaɗa jita-jita. Ta kuma tabbatar da kyakkyawar alaƙa da fahimta da ke tsakaninta da Gwamnan da gwamnatin sa, tare da buƙatar al’umma su ci gaba da nuna haɗin kai da mutunta al’adunsu.
Hawan Daushe dai wani muhimmin biki ne da ake gudanarwa a lokacin Sallah, inda Sarakuna da masu riƙe da muƙamai ke hawan dawakai tare da baje kolin al’adun gargajiya. Wannan hawan na taka rawa wajen ciyar da al’adu gaba da kuma ƙarfafa haɗin kan jama’a a jihar Bauchi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp