Majalasin Kwamitin Dalibai na Masallacin Juma’a na Imam Dakta Idris Abdul’azeez Dutsen Tanshi Bauchi, sun gargadi jama’a ko kungiyoyin addini cewa kada wani ko wasu su fito domin yin zanga-zanga ko yin wani abu da ka iya janyo tashin hankali a cikin al’umma sakamakon tura malamin nasu zuwa gidan yari da kotu ta yi.
Idan za a ku tuna dai a ranar Litinin ne kotun Majistire ta 1 ta aike da fitaccen malamin zuwa gidan gyaran hali biyo bayan gurfanar da shi da ‘yansanda suka yi kan zargin ‘Tada Zaune Tsaye – Tada Hankalin Jama’a’.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tasa Ƙeyar Dr. Idris Kan Zargin Kalaman Batanci Ga Manzon Allah
- Yadda Furucin Dakta Idris Kan Manzon Allah Ya Janyo Zafafan Muhawara A Bauchi
A wata sanarwar manema labarai suka samu daga majalasin malamin ya fitar dauke da sanya hannun shugabanta, Malam Ya’u Idris, ya ce, ‘yansanda sun gayyaci malamin nasu ne domin amsa tambayoyi kan korafin da kungiyar Fitiyanul Islam ta shigar a kansa.
Sanarwar na cewa, “A madadin Majilsin Kwamitin Dalibai na Masallacin Juma’a na Imam Dr. Idris Abdul’azeez Dutsen Tanshi Bauchi, suna shaidawa daukacin Jam’a bisa gayyatar da aka yi wa Malam da hukumar ‘yansanda ta Jihar Bauchi karkashin Kwamishina ta yi, dangane da neman wasu bayanai akan korafin da ‘yan Fitiyanu Islam na Tijjaniyya suka yi na zargin “tada hankalin jama’a”.
“Imam Dr. Idris Abdul’azeez Bauchi ya amsa gayyata ce kawai ta hukumar ‘yansanda ta Jihar Bauchi.
“Kada wasu jama’a ko kungiyoyi na addini da sauransu su fito don yin zanga-zanga ko tashin hankali akan abin da ya faru.
“Sakamakon haka muna kara shaidawa jama’a da su zauna lafiya, da cigaba da yin addu’a kamar yadda aka saba, saboda maganar tana gaban Kotu kuma ana kokari bisa hanyar Shari’a.”
Sanarwar ta ce, a halin da ake ciki a yanzu Malamin nasu yana cikin koshin lafiya da yanayi mai kyau.
“Muna kara jaddadawa duk wata kungiya ko ta addnini ko ba ta addini ba da ka da su dauki doka a hannunsu kan abin da ya faru, sun yi hakan ne bada amincewar Majlis ba ko shi Malam ba. Muna addu’a Allah ya kara daukaka Sunnah da Tauhidi.”