Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da hannu a kara farashin man fetur da aka yi a ranar Laraba.
A ranar Laraba ne, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), ya kara farashin man fetur daga Naira 897 zuwa Naira 1,030 a Abuja; daga Naira 855 zuwa Naira 998 a Legas; sannan farashin ya bambanta a wasu sassan na kasar.
- Gwamnatin Sakkwato Za Ta Karshe Miliyan 95.4 Domin Gyara Masallatan Juma’a
- Dorewar Bunkasuwar Tattalin Arzikin Sin Ta Karawa Duniya Kwarin Gwiwa
Wannan ya sa jama’a suka fara nuna damuwa, inda da dama suka bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi kokarin dawo da tsohon farashin.
Da zanta wa da jaridar Daily Trust, Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin ba ta da alhaki kan karin farashin.
Ya bayyana cewa NNPCL ce ta yanke shawarar karin farashin saboda yanayin kasuwar makamashi, ba tare da wani umarni daga gwamnati ba.
Ya kara da cewa, bisa tanadin Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA), gwamnati ba za ta iya saita farashin man fetur ba.
Ministan ya bayyana cewa tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayu 2023, NNPCL tana bin matakai don kiyaye farashin, amma yanzu ba za ta iya daukar asara ba.
Ya ambaci manyan dalilai guda biyu da ya sa aka samu karin farashin: rikicin Gabas ta Tsakiya da rashin tabbas da ta mamaye kasuwar man fetur ta duniya.
Bugu da kari, NNPCL a matsayin kamfani mai zaman kansa ba zai iya ci gaba da daukar asara ba.
Ya roki ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yin hakuri, inda ha tabbatar da cewa farashin man zai sauko nan gaba.
Ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da amfani da kudin da ta samu daga cire tallafin man fetur don inganta bangarorin kiwon lafiya, ilimi, gine-gine, da tsaro.
Ministan ya kuma ambaci cewa jarin da gwamnati ta fara zubawa a harkar gas zai taimaka wajen rage tasirin karin farashin man fetur din.