Ƙungiyar dilallan man fetur masu zaman kansu ta kasa (IPMAN), ta musanta yunkurin kara farashin man fetur zuwa N700 kan kowace lita.
IPMAN ta musanta shirin ne cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Asabar.
- Za Mu Sake Neman Lashe Gasar Firimiya – Kocin Arsenal
- Sallah: Yadda Sarkin Gombe Ya Jagoranci Hawan Daba
Sun ce farashin mai a yanzu yana tafiya ne kan farashin kasuwa, kuma an yi hasashen kara kudin man ne saboda darajar Naira da ke sama tana kasa a kasuwar canji.
NAN ta ruwaito cewar wasu ‘yan kasuwa sun yi hasashen tashin farashin man ne zuwa naira 700 kan kowace lita, sabanin yanzu da yake 540, da zarar ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun fara shiga da man cikin kasar a watan Yuli.
Sun yi hasashen ne bisa farashin da kasuwa ta yi wa naira a yanzu da kuma kudin sauke man a Nijeriya.
Darajar naira ta ragu a ranar Juma’a zuwa N769.25 kan dala daya a kasuwar canji, bayan Shugaba Bola Tinubu ya janye tsarin kayyade farashin naira da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke yi a baya.
Hakan na nufin darajar naira ya ragu da kashi 0.82 cikin 100 idan aka kwatanta da N763 da aka canzar da ita kafin fara bikin Babbar Sallah a ranar Laraba.
Tuni dai dubban mutane suka fara korafi a kafafen sada zumunta kan yiwuwar tashin farashin man fetur din.