Gwamnatin Jihar Sakkwato ta buƙaci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ya riƙa bin diddigin gaskiyar labari kafin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka shafi ƙasa baki daya.
Da take mayar da martani kan gargaɗin da Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi a taron da aka gudanar kan samar da tsaro a yankin Arewa maso yamma a Jihar Katsina a ranar Litinin, gwamnatin jihar Sakkwato ta ce ya kamata Mataimakin Shugaban Ƙasa ya tuntubi Gwamna Ahmed Aliyu domin tabbatar da labarin da ya yi tsokaci kan zargin shirin tsige Sultan Muhammadu Sa’ad ll.
- Gwamnatin Sakkwato Na Shirin Warware Rawanin Sarkin Musulmi – MURIC
- Babu Mai Taɓa Sarkin Musulmi – Kashim Shettima
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Abubakar Bawa ya sanya wa hannu, ya bukaci Mataimakin Shugaban Ƙasa da ya nemi cikakken bayanin al’amuran da suka shafi ƙasa baki ɗaya kafin yin tsokaci a kan wani abu.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce a gaskiyar lamari babu wani shiri na tube rawanin Sarkin Musulmi, haka kuma ba su aike masa da wata barazana ba.
Gwamnatin ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin kare martabar Masarautar a kowane lokaci.