Gwamnatin tarayya ta nuna rashin gamsuwarta da yadda aikin kwangilar babbar hanyar Yola zuwa Mubi, da kamfanin ‘AG Bision Nigeria Limited’, ke gudanarwa a kan zuzurutun kudi har naira miliyan dubu 21 da miliyan takwas.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da ministan ma’aikatar sufuri, Mustapha Shehuri, suka nuna rashin gamsuwar lokacin da suke rangadin duba ayyukan da gwamnatin tarayyar ta bayar a jihohin Adamawa da Taraba.
Shekaru biyar kenan da gwamnatin ta ba da aikin babbar hanyar Yola zuwa Mubi ga Kamfanin ‘AG Bision Nigeria Limited’, sai dai ko kashi guda bisa ukun aikin ba a yi ba.
Sakataren gwamnatin tarayyar ya kuma kalubalanci dan kwangilar hanyar da cewa ko a zaman da aka yi da shi, ya bayyana jinkirin da aikin ya samu da matsalar tsaro. Ya ci gaba da cewa hukumomi ba su ji dadin yadda aikin yake ke gudana ba, domin matsayar da suka tsaya da dan kwangilar shi ne ya koma bakin aiki.
“Mun kawo batun kudade a zaman, amma ba na tsammanin ita ce ke kawo jinkirin aikin, domin mun tabbatar ma’aikatar sufuri ta yi duk mai yiwuwa, domin biyan kudaden.
“Dole ne dan kwangila ya kara himma kan aikinsa ta hanyar kammala aikin, saboda aikin ya wuce wa’adin da aka yi alkawarin za a gama.
“Za mu ci gaba da matsa wa dan kwangilar har sai mun ga ya dauki matakin yin abin da ya kamata,’ in ji Boss Mustapha.