Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa, sojojin da aka tura fadar Sarki da ke unguwar Nasarawa a Kano ba sun je ne don aiwatar da duk wani umarnin kotu a rikicin masarautar ba.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga rahotannin da kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA), reshen jihar Kano ta buga da wata jarida ta yanar gizo (ba JARIDAR LEADERSHIP ba) a ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu, 2024, wanda ta zargi sojoji da ɓangarenci kan rikicin masarautar a Kano.
- Gwamnoni 9 Da Har Yanzu Ba Su Babe Da Iyayen Gidansu Ba
- Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa A Tsaya Kan Umarnin Kotu Kan Rikicin Sarki 2 A Kano
Ya ce, saɓanin rahoton, sojoji sun ɗauki matakin ne kawai da zummar daƙile duk wata matsala ko taɓarɓarewar tsaro da rikicin masarautar Kano zai iya haifarwa.
Kakakin Rundunar Sojin ya ce, “Batun da ya shafi rundunar Sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro shi ne hana taɓarɓarewar doka da oda a jihar, wanda wasu ɓata gari ka iya amfani da damar don musgunawa jama’a.
Ya ce, Sojoji za su shiga tsakani cikin gaggawa muddin suka fahimci cewa lamarin tsaron zai gagari ‘yansanda.
Ya kara da cewa, duk kokarin da Sojoji ke yi a wannan mataki shi ne, sanya ido kan lamarin da kuma kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana idan lamarin ya ta’azzara da zai kawo barazana ga tsaron jihar da ma yankin baki daya.