Hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC, ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo na cewa, ta umarci masu hidimar bautar ƙasa da su gyara asusun ajiyarsu dan shirin karɓar alawus din naira ₦70,000 da za a fara biyansu duk wata.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar mafi karancin albashin ƙasa na naira ₦70,000 a watan da ya gabata, ga ma’aikata a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu wanda ya kasance ma’auni na alawus ɗin wata-wata da masu hidimar ƙasa ke samu.
- Ko Zuwan Mbappe Zai Dusashe Tauraruwar Bellingham A Real Madrid?
- Gwamna Yusuf Ya Jaddada Ƙudirinsa Na Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa A Kano
Daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a na NYSC, Eddy Megwa, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ƙaryata labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta game da sabon alawus din tare da kira ga masu hidimar ƙasar da sauran jama’a da su sani, cewa hukumar ba ta sami umarni daga kowane bangaren gwamnati da ke da alhakin albashi ba.
Eddy Megwa, ya buƙaci masu hidimar ƙasar da su daina barin masu yaɗa labarun ƙanzon kurege suna wasa da hankalinsu tare da gargaɗi ga masu shafukan yanar gizo da na sada zumunta da su daina fitar da bayanan da suka shafi hukumar NYSC ba tare da izini ba.