Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki, ta ce ba ta san dalilin da ya sanya ‘yan Nijeriya ke son gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan ba.
Da yake jawabi shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar, kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala wani taro da gwamnonin suka yi a Abuja.
- Mangal Ya Dauki Nauyin Yi Wa Masu Ciwon Mafitsara 80 Aiki A Katsina
- Da Mu Za A Yi Zanga-zangar Matsin Rayuwa – NLC
“Ba mu san dalilin da ya sanya aka shirya gudanar da zanga-zanga a fadin Nijeriya ba, kuma ba mu san a kan me masu shirya zanga-zangar za su gudanar ba.
“Mun gayyaci masu shirya gudanar da zanga-zangar domin mun tattauna da su, mu ji dalilinsu na shirya wannan zanga-zangar, domin mu cimma matsaya.”
A cewarsa, a matsayinsu na gwamnoni sun iya bakin kokarinsu wajen ganin, komai ya tafi yadda ya kamata a kasar nan ta hanyar magance matsalolin tsaro, farfado da tattalin arziki, tare kuma da samar da ayyukan yi ga matasa.
Kazalika, ya kara da cewa baya ga irin wannan kokari da suke yi bai ga dalilin gudanar da wata zanga-zanga a wannan lokaci ba.
Ana sa ran fara zanga-zangar ne a ranar 1 ga watan Agusta, wadda za ta dauki tsawon kwanaki 10 ana yi.
Masu shirya zanga-zangar na son amfani da wannan damar wajen jan hankalin gwamnati kan halin matsin rayuwa da ake ciki a Nijeriya, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma tashin dalar Amurka da wasu sauye-sauye da aka kawo.