Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya danganta faduwar da APC ta yi a jihar Osun da aka gudanar da rikicin cikin gida da ya mamaye jam’iyyar a jihar.
Adamu ya sanar da cewa, rikicin cikin gida a tsakanin masu ruwa da tsaki a APC reshen jihar ne ya janyo faduwar jam’iyyar a zaben na gwamna a jihar Osun.
- Kasar Sin Za Ta Tsaya Kan Manufar Bude Kofarta Ga Duniya
- Babu Abin Da Zai Kawo Min Cikas Wajen Inganta Rayuwar Jama’a – Sadiya Farouq
A cewar Adamu, “Mun sha kasa ne a zaben ba wai don ba za mu iya lashe zaben ba, amma sai saboda rikicin cikin gida na APC a jihar.”
Shugaban wanda ya sanar da hakan a hirarsa da sashen Hausa na BBC, ya ci gaba da cewa, “Muna da dimbin magoya baya a ‘yan kwanaki kafin a gudanar da zaben, babu wanda ya taba tunanin cewa za a kayar da mu a zaben.
“Mun amince mun sha kasa a zaben kuma hakan, ya zamo mana darasi.”
Ya jaddada cewa, ko kusa kayar da jam’iyyar a zaben jihar Osun ba zai zamo musu wata alamar rashin samun cin nasara a zaben kakar 2023 ba, domin sun fadi ne kawai a jiha daya daga cikin jihohi 22.