A wani fefen bidiyo da yake yawo, wanda bai wuce minti goma ba, an jiyo Sanatan Kano ta Kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila, na shaguɓe ga wanda suke sukarsa ko kuma nuna ko in kula da tafiyar Kwankwasiyya NNPP da suke zargin ba ya yi mata komai.
Sanatan ya yi martani tare da nuna irin gudunmawar da ya bayar wajen ganin sun taimakawa tafiyar tun daga farkonta har zuwa wannan lokacin.
- Ba Za Mu Lamunci Dauki-Dora A Shugabancin Majalisa Ba —Kawu Sumaila
- Kudaden ‘Yan Majalisa: Wa Za A Gaskata Tsakanin Hukumar Albashi Da Kawu Sumaila?
Sanatan ya ce “Ku kyale duk masu cewa ba mu yi wa wannan gwamnatin komai ba, Allah ne shaida tun daga zaɓe har zuwa kotu, mun yi abinda zamu iya, kuma sillarmu Allah ya ƙarfafi wannan tafiyar a wannan yankin”
Sanatan ya ce a yanzu ba shi da wani abu da wuce ace ya sauke nauyin da al’ummar Kano ta kudu suka ɗora masa na ganin ya wakilce su a zauran majalisar Dattijai.
Wannan na zuwa ne yayin da maganganu suka fara yawa kan cewa sanata na samun saɓani ko kuma an raba gari tsakaninsa da madugun Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ko a baya-bayan nan ma dai an jiyo mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin-Tofa na jaddada ba su da wani saɓani tsakaninsu da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Tofa da Rimin-Gado, Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe.
Sanata Kawu Sumaila da Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe da kuma tsohon kakakin majalisar Jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum, suna da tasiri a siyasar kano ta kudu, wanda ake ganin ficewarsu daga Jam’iyyar APC a lokacin zaɓen 2023 ne ya janyo wa jam’iyyar gagarumar asara a yankin.