Sabon dan wasan tsakiyar Manchester United, Casemiro, ya bayyana cewa ba son kudi ne ya sa ya yanke shawarar komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ba duk da rade-radin da ake yi na cewa kudi yabi.
A ranar Litinin Manchester United ta gabatar da Casemiro a matakin sabon dan kwallon da ta dauka a bana daga Real Madrid a gaban magoya bayanta a filin wasa na Old Trafford gabanin wasan kungiyar da Liverpool.
Dan wasan dan Brazil, wanda ya yi ban kwana da kungiyar Sifaniya a ranar ta Litinin, ya kalli karawar da Manchester United ta doke Liverpool 2-1 a wasan Premier League kuma wasan farko kenan da kungiyar ta yi nasara a bana, karkashin sabon mai koyar da kungiyar, Erik ten Hag, bayan da ta sha kashi a hannun Brighton da Brentford.
Dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 30 ya ce ya koma daya daga babbar kungiya a fannin kwallon kafa a duniya, yana da sha’awar daukar Premier League da ragowar kofunan da kungiyar zata buga.
Manchester United ta sayi dan wasan kan yuro miliyan 70, kan yarjejeniyar kakar wasa hudu, wanda zai zama ‘yan gaba-gaba masu karbar albashi kuma shi ne dan wasa na uku da Real Madrid ta sayar mafi tsada a tarihin kungiyar, bayan Cristiano Ronaldo da Angel Di Maria.
Casemiro ya koma Sifaniya da buga wasa daga Sao Paulo a shekarar 2013, inda ya dauki Champions League biyar a Real Madrid da La Liga uku da Cope del Rey daya, sannan ya buga Champions League a bara da Real ta doke Liverpool ta lashe kofin Zakarun Turai na 14 jumulla, wanda ya yi mata wasa 336.
Kawo yanzu United ta dauki ‘yan kwallo da suka da hada da Tyrell Malacia daga Feyenoord da Christian Eriksen, wanda kwantiraginsa ya kare a Brentford da kuma Lisandro Martinez daga Ajad.
Jerin ‘yan wasa 10 da Real Madrid ta sayar da tsada a tarihi
1. Cristiano Ronaldo Kakar wasa: 2018 zuwa 2019, Kungiyar da ta dauke shi: Jubentus
Gasar da ya koma bugawa: Serie A, Kudin da aka sayar da shi: Yuro miliyan 117.00 2. Angel Di Maria.
Kakar wasa: 2014 zuwa 2015. Kungiyar da ta dauke shi: Manchester United. Gasar da ya koma buga wa: England Premier League. Kudin da aka sayar shi: Yuro miliyan 75.00
3. Casemiro, Kakar wasa: 2022 zuwa 2023. Kungiyar da ta dauke shi: Manchester United. Gasar da ya koma bugawa: England Premier League. Kudin da aka sayar da shi: Yuro miliyan 70.65. 4. Albaro Morata. Kakar wasa: 2017 zuwa 2018. Kungiyar da ta dauke shi: Chelsea. Gasar da ya koma bugawa: England Premier League. Kudin da aka sayar da shi: Yuro miliyan 66.00. 5. Mesut Ozil, Kakar wasa: 2013 zuwa 2014. Kungiyar da ta dauke shi: Arsenal. Gasar da ya koma bugawa: England Premier League. Kudin da aka sayar da shi: Yuro miliyan 47.00 6. Mateo Kobacic Kakar wasa: 2019 zuwa 2020, Kungiyar da ta dauke shi: Chelsea Gasar da ya koma bugawa: England Premier League. Kudin da aka sayar da shi: Yuro miliyan 45.00. 7. Achraf Hakimi. Kakar wasa: 2020 zuwa 2021. Kungiyar da ta dauke shi: Inter Milan, Gasar da ya koma bugawa: Serie A. Kudin da aka sayar shi:Yuro miliyan 43.00 8. Robinho. Kakar wasa: 2008 zuwa 2009. Kungiyar da ta dauke shi: Manchester City, Gasar da ya koma buga wa: England Premier League. Kudin da aka sayar da shi: Yuro miliyan 43.00. 9.
Raphael Barane. Kakar wasa: 2021 zuwa 2022, Kungiyar da ta dauke shi: Manchester United. Gasar da ya koma bugawa: England Premier League. Kudin da aka sayar da shi: Yuron miliyan 40.00. 10. Gonzalo Higuain, Kakar wasa: 2013 zuwa 2014. Kungiyar da ta dauke shi: Napoli. Gasar da ya koma bugawa: Serie A Kudin da aka sayar da shi: Yuro miliyan 39.00