Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa, nasarar zabe ba wai a yawan kuri’un da aka kada ba ne kawai, har da bin dokokin da aka gindaya wa zaben.
Doguwa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidan Talabijin na Channels TV yayin da yake mayar da martani kan cece-kucen da ake tafkawa dangane da zaben 2023 a jihar Kano.
- Da Ɗumi-Ɗumi: Jam’iyyar APC Ta Kori Shugabanta Na Jihar Bauchi, Aliyu Misau
- NNPP Ta Nemi EU, Amurka Da AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano
Ya ce zabuka a tsarin dimokuradiyya irin na Nijeriya a kodayaushe suna kan tsari da bin ka’idoji, kuma tsayawa zabe bisa wadannan ka’idoji ne ke sa a samu sahihin zabe.
Ya ce, “A gare ni idan ka tambaye ni abin da ke faruwa a Kano, zan ce, abin da ya saba faruwa ne, Kano jiha ce mai ci gaba da tasiri ta fuskar siyasa da akida.
“Abin da wasu daga cikin mutanenmu suka gaza fahimta shi ne, zabuka musamman a tsarin dimokuradiyya irin wacce ake gudanarwa a Nijeriya, ta rataya kan bin ka’idojinta (siyasa), ba wai kawai na ci zabe ba ne (da yawan kuri’u).” Inji Doguwa