Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ya bayyana cewar bankin ba zai kara wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudi ba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron tattaunawa na musamman a ofishin babban bankin na Jihar Legas, inda ya ce tuni CBN da sauran masu ruwa da tsaki suka fara duba wuraren da ake samun matsin lamba game da canjin kudin.
- Ganau Ya Yi Karin Haske Kan Kisan Makiyaya 37 A Nasarawa
- Canjin Kudi: Ina Sane Da Wahalar Da Mutane Ke Sha, Komai Zai Daidaita – Buhari
“Na tabbatar mutane cewa ba zamu kara tsawaita wa’adin daina karbar kudin ba.
“Mun duban wuraren da ake samun tsaiko kuma muna yin duk mai yiwuwa don magance matsalolin da ake fuskanta.”
Wannan dai na zuwa ne bayan da CBN ya kara tsawaita wa’adin daina karbar tsofaffin kudi daga ranar 31 ga watan Janairu, zuwa 10 ga watan da muke ciki.
Sai dai gwamnonin APC da suka gana da Buhari a ranar Juma’a, sun bukaci shugaban da ya sanya baki a kan a ci gaba da karbar tsofaffin kudin.