Zababben Sanata mai wakiltar shiyyar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewa ‘yan majalisar tarayya ba za su lamunci duk wani shirin dauki-dora na shugabanni da jam’iyyar APC mai mulki ke shirin yi musu a zauren majalisar ba.
Kawu Sumaila, wanda ya kasance dan jam’iyyar adawa ta NNPP a zauren majalisar, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa da manema labarai a Abuja.
- Matsalar Ruwan Sha: Yara 9 Sun Mutu A Kwale-Kwale, 12 Sun Bace A Zamfara
- Yadda Muka Yi Da ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Iyalina – Sarkin Kagarko
A cewarsa, sun fara ganin jam’iyya mai mulki ta bayyana cewa ta ware wata shiyya da sunan neman mika mata ragamar shugabancin zauren majalisar a karo na 10, wanda shi ne abinnda suka fara gani a dimokuradiyya, amma su da suke da jinin wannan majalisar, ba za su taba bari wannan abu ya faru ba.
Sanatan, ya kara da cewa dole ne sai sun ce a’a game da wannan al’amarin domin kada tarihi ya zo a ci gaba da yin irin hakan, kuma za su tsaya tsayin-daka wajen ganin sun tabbatar da wannan abu bai yiwu ba, idan Allah Ya so ya yarda.
Ya ce, “Wannan al’amarin shi ne ya sake nuna cewa mun sake dawowa mulki irin na danniya na soja, amma idan salon mulki irin na dimokuradiyya muke koyi, to, muna da bangarori guda uku, wanda su ne na zartarwa, na majalisa dana shari’a wanda kowane gashin kansa yake ci.
“Amma idan za a yi irin wannan magana, sai kowane ya je ya yi a bangarensa, amma bawai bangaren zartarwa su shiga cikin bangaren majalisa ba ko wani bangare ya yi kutse a cikin lamarin wani bangare ba.
“Hikima na yin irin wannan a kan duk wani shugaba mai cikakken iko shi ne, domin a samar da wani gurbi wanda za a rika tankwashe kafar shugaban kasa idan ya mike, to amma idan aka ce shi shugaban kasar ne da kan shi zai nada ma zauren shugabanni, to ba za a samu irin biyan bukatun da ake bukata ba.
“Sannan duk mun taho da bukatun mu iri daban-daban, kana ga irin abubuwan da suke ta faruwa a Nijeriya wanda mutane ke bukatar a sauya musu fasalin kasar ko a duba yanayin tsarin mulkin baki daya domin a gyara shi, ko kuma a yi cikakken tsari domin kowace juha ta rika rike kudinta da kanta, to abu mafi sauki ga mutanen da suka zo da irin wannan tunanin shi ne a bar su s uzo su zauna a karkashin zaure daya domin yan Nijeriya za su fi yarda da su.
Kawu Sumaila ya ci gaba da cewa, APC ba ita ba ce Nijeriya a bisa wasu dalilai guda biyu, inda ya bayyana cewa na daya ita ce, a cikin wannan majalisar ta 10, jam’iyyar APC tana da kashi 50 na ‘yan majalisa 59 daga cikin 109, yayin da sauran ‘yan adawa suna da kashi 55.
“Haka zalika a cikin daya zauren majalisar, jam’iyyar APC ba ta da rinjaye a ciki domin ‘yan adawa sun fi yawa.
“Abu na biyu shi ne, akalla mutane miliyan 90 da wani abu ne suka yi rajistar zabe a kasar nan, mutane miliyan 80 da wani abu ne suka karbi katin zabensu, amma karshe mutane miliyan 23 da wani abu ne suka je suka yi zabe, sannan a cikin mutum miliyan 23 da suka kada kuri’a, APC tana da miliyan takwas ne kacal, yayin da sauran jam’iyyun suna da sauran kuri’un.
“Wato hakan ke nuna cewa ‘yan Nijeriya sun bar ‘yan siyasa ne da halinsu domin ba su yarda da su ba saboda gani suke yi kowa irin jiya ne idan an dawo kuma wannan shi ne lokacin da ya kamata a ce an samar da gyara sama da kowane lokaci domin wanda ya zama shugaban kasa a APC, mutum ne wanda ya yi gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya a kasar nan.
“Har ila yau, sabon zababben shugaban kasar, mutum ne da ya jagorance mu a zama daban-daban kuma ya koya mana na ki har ya shiga jikinmu ta yadda duk mutumin da ya zo ya ce mana a’a, sai mu ce masa na ki don shi ya koya mana na ki.
“Yanzu ba zancen fada ko tashin hankali ba ne, illa ranar zaben shugabannin majalisar kawai za a shiga zaurorin nan a je a yi zabe domin a zabi wanda ake so saboda kowa ya cancanta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya fada tare da na dokokin majalisar.” in ji shi
A karshe, Sanatan, ya nuna cewa za su zabi wanda suke so, kuma kowa ya san gaskiya ba wai ‘yan adawa kawai ba, kana sun tabbatar da cewa za a zabi sabbin shugabanni kuma za su fito ne daga cikin jam’iyyar APC mai Mulki.