• English
  • Business News
Saturday, July 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Za Mu Saka Addini A Tsarin Kidayar 2023 Ba —NPC

by Sadiq
2 years ago
in Labarai
0
Ba Za Mu Saka Addini A Tsarin Kidayar 2023 Ba —NPC
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta musanta labarin da ake yadawa cewa za a yi tambayoyi game da Addini a lokacin kidayar da za a gudanar a watan Mayu.

Ana ta yada wani sakon murya a manhajar Whatsapp da ake kira ga Musulmai da su sani cewa za a tambaye su game da addininsu a matsayin wata hanya ta rage musu yawa a kidayar da ke tafe.

  • Kungiyoyin Arewa Sun Yi Fatali Da Bukatar Sakin Nnamdi Kanu
  • Za Mu Ceto Mutanen Da Aka Sace A Zamfara —’Yan Sanda

Sai dai a sanarwar da daraktan watsa labarai na NPC Isiaka Yahaya ya fitar, ya ce bidiyon na bogi ne kuma ba su da wani shiri mai kama a lokacin gudanar da kidaya.

Ya tabbatar da cewa hukumar ta kidaya ba za ta yi wata tambaya da ke da alaka da Addini ba.

“An dauki matakin cire batun Addini da kabila daga takardar kidayar ne domin irin tsaurin da wadannan batutuwa ke da shi a Nijeriya da kuma kare kidayar daga ce-ce-ku-cen da ba shi da amfani,” in ji hukumar.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Hauhawar Farashin Kayan Abinci Ya Ragu A Nijeriya

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

Haka kuma hukumar ta ce ta bi diddigi ta gano cewa an soma aikawa da wannan sakon ne a manhajar Whatsapp a lokacin kidayar da aka yi a Ghana a 2021.

Ta kuma ce an soma yada wannan sakon a Nijeriya a lokacin da aka yi gwajin kidaya a watan Yulin 2022.

An soma kidayar jama’a bayan samun ‘yancin kan Nijeriya ne a 1962 inda aka kididdige cewa jama’ar kasar sun kai miliyan 45.5.

Kidaya ta karshe da aka yi a kasar an yi ta ne a 2006 inda aka kididdige cewa akwai sama da mutum miliyan 140 a kasar, sa’annan a 2019 kuma hukumar ta yi hasashen cewa jama’ar kasar sun haura mutum miliyan 200.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KidayaNPC
ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Sanda Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Ceto Mutane A Adamawa

Next Post

An Bude Bikin Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Kasa Da Kasa Na Kasar Sin Karo Na 3

Related

sallah
Labarai

Yadda Hauhawar Farashin Kayan Abinci Ya Ragu A Nijeriya

5 minutes ago
Fyade
Rahotonni

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

3 hours ago
APC
Manyan Labarai

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

4 hours ago
A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya
Labarai

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

15 hours ago
Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano
Labarai

Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba

16 hours ago
Kasar Sin Ta Nuna Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Nijeriya Buhari
Labarai

Za A Dinga Tunawa Da Buhari A Matsayin Waliyyi A Siyasar Nijeriya —Dakta Zangina

17 hours ago
Next Post
An Bude Bikin Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Kasa Da Kasa Na Kasar Sin Karo Na 3

An Bude Bikin Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Kasa Da Kasa Na Kasar Sin Karo Na 3

LABARAI MASU NASABA

sallah

Yadda Hauhawar Farashin Kayan Abinci Ya Ragu A Nijeriya

July 19, 2025
Shettima

Nijeriya Za Ta Rika Samun Naira Tiriliyan Uku A Aikin Tatsar Rogo Duk Shekara – Kashim

July 19, 2025
Fyade

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

July 19, 2025
APC

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

July 19, 2025
Dangote

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

July 18, 2025
Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

July 18, 2025
2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

July 18, 2025
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

July 18, 2025
majalisar kasa

Kirkirar Sabbin Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Dabaibaye Sauraron Jin Ra’ayoyin Gyaran Tsarin Mulki

July 18, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

July 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.