Sabuwar ministar ma’aikatar yawon bude ido, Misis Lola Ade-John, ta ce za ta yi aiki tare da ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki don mayar da bangaren yawon bude ido ya zama babban hanyar samun kudaden shiga ga Nijeriya.
Ade-John ta bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ganawarta da gidan rediyon Nijeriya a Abuja jim kadan bayan kama aiki a ma’aikatarta.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rahoto cewa Ade-John ta samu tarba daga babban sakatariyar ma’aikatar yada labarai da al’adu, Dr Ngozi Onwudiwe da shugabannin hukumomi da sassan ma’aikatar.
Ministar, ta ce yawon bude ido ya kunshi kasuwanci da hada kai da masu ruwa da tsaki, inda ta sake nanata cewa, za ta hada kai da masu zuba jari, da gwamnatoci, da jama’ar gari domin inganta fannin.