Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), CGI Isah Jere Idris, ya shaida cewar, ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da cewa hukumarsa na gudanar da ingataccen aiki ga al’ummar Nijeriya a kowani lokaci ba.
Jere Idris ya shaida hakan ne a wajen bikin kaddamar da ofishin aikin Fasfo a Abeokuta, inda yake cewa, aikin ya zo a kan gaba domin bunkasa aikin samar da Fasfo cikin hanzari da sauki ga al’ummar Ogun.
A sanarwar da Kakakin hukumar, DCI Tony Akuneme ya fitar a ranar Alhamis, Mr Jere ya yaba wa gwamnati da al’ummar jihar a bisa hadin kai da goyon bayan da suke ba su wajen gudanar da ayyukansu domin tabbatar da cigaban kasa a kowani lokaci.
Daga bisani Shugaban hukumar y kai ziyarar aiki wa gwamnan Jihar Ogun, Dakta Dapo Abiodun da Basaraken gargajiya Alake na Egbaland Oba Adedotun Gbadebo III dukka domin kyautata aiki da samun karin hadin kai.
Sannan ya kuma ziyarci wasu iyakokin da suke jihar inda ya gana da masu ruwa da tsaki kan bukatar hada karfi da karfe domin wayar da kai kan tsaro a daidai lokacin da ake fuskantar babban zaben 2023.
CGIS ya kuma ziyarci ofisoshin sintiri na hukumar guda hudu da suke shiyyar a jihohin Legas da Ogun gami da zuwa ofisoshin yin Fasfo da suke Ikoyi da Alausa tare da sabon ofishin yin Fasfo da ke Alimosho wanda ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola zai kaddamar da fara amfani da shi kwanan nan.
Sannan kuma Jere ya ziyarci Basaraken Oba da ke Legas, Oba Akiolu da na Oniru da ke Legas daga bisani ya koma Abuja domin cigaba da aikin kula da shige da fice.