Kungiyar Kabilun Kudancin Jihar Kaduna (SOKAPU), ta ce a zaben 2023 sam ba za ta taba sabuwa a sake yin tsarin zabar musulmai biyu a matsayin gwamna da mataimaki ba.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Luka Binnyiyat, ta fitar a jihar ta ce ba zasu sake marawa ‘yan addini daya baya ba.
- An Yi Jana’izar Babban Sakataren kungiyar OPEC, Muhammad Sanusi A Yola
- Idan Na Zama Shugaban Kasa Yajin Aikin ASUU Zai Zama Tarihi – Kwankwaso
Luka na mayar da martani ne kan yadda dan takarar gwamna a jihar a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki a jihar Sanata Uba Sani, ya wallafa a shafinsa sada zumunta na facebook a ranar Litinin, na tabbatar da daukar Mataimakiyar Gwamna jihar mai ci a yanzu, Dakta Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa.
Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yi ammana da cewa, a bangarorin biyu na jihar akwai Kiristoci da Musulmai da suka cancanta wanda kuma suka fi dace wa a dauka a matsayin mataimaka a kowace jam’iyyar siyasa.
A cewar sanarwar gwamna El-rufai na sane da cewa yawan al’ummar da ke a kudancin kaduna ba su kai yawan adadin Kiristocin da ke a yankin ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ba wai muna kin jinin Dakta Hadiza bane, amma ya kamata a yi adalci kuma sake daukarta a matsayin mataimakiya kamar cin fuska ne a gare mu.”