Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang, ya ƙaryata labaran da ke yawo cewa yana shirin barin jam’iyyar adawa ta PDP domin komawa jam’iyyar APC mai mulki.
A kwanakin baya, wasu jaridu sun ruwaito cewa yana cikin gwamnoni da ke shirin sauya sheƙa daga PDP saboda rikicin da ke faruwa a cikin jam’iyyar.
- An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa
- An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin
Amma a wata hira da ya yi da BBC, Gwamna Muftwang ya ce babu gaskiya a cikin wannan magana.
Ya ce wani abokinsa ya turo masa da labarin, amma sai ya faɗa masa cewa ba a hana mai farauta neman namun daji.
Ya ce ya tabbata sun ga wani abin sha’awa a cikin jam’iyyarsu ta PDP, shi ya sa suke ganin idan ya shiga APC zai kawo musu tagomashi.
Ya ce kamar yadda mutane suka karanta a jarida, shi ma ya karanta, amma babu gaskiya cikin batun.
Ya ce a yanzu, kowa ya san yana cikin PDP kuma yana da matsayi a jam’iyyar, bai bar ta ba kuma da yardar Allah zai ci gaba da zama a cikinta.
Ya ce dalilin da ya sa wasu ke son ya koma APC shi ne domin jam’iyyar APC a Filato ba ta da shugabanni nagari, shi ya sa suke kallon shugabannin PDP da fatan su shiga jam’iyyar domin kawo gyara.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mambobin APC na ƙasa suna sha’awar abubuwan da PDP ta yi a Filato, kuma suna ganin irin waɗannan ayyuka na buƙatar shugabanni masu nagarta.
Amma ya ce su dai suna sa Allah a gaba a siyasa da kuma a cikin jama’a, kuma duk inda Allah Ya nufa da inda jama’a suke so su tafi, to a can ne za su tafi.
Game da rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi, gwamnan ya ce yanzu an sasanta matsalolin.
Ya ce an yi zama na musamman da na haɗin kai domin kawar da bambance-bambancen da suka jawo rabuwar kawuna.
Ya ce kusan shekara guda suna fama da wannan rikicin, amma yanzu da yardar Allah an wuce wannan mataki.
Ya ce shugabanni da magoya bayan jam’iyyar sun yi farin ciki da zaman da aka yi, kuma suna fatan rikicin ya zama tarihi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp