Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake nanata cewa zaben 2023 mai zuwa zai kasance cikin gaskiya da gaskiya domin ba zai bari a magudi ta kowace hanya ba.
Shugaban ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake karbar bakuncin tawagar Kungiyar Dattawan Afrika ta Yamma kafin zabe, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Saliyo, Dakta, Ernest Bai Koroma a fadar gwamnati da ke Abuja.
- Hisbah Ta Kama Motoci 3 Makare Da Giya A Kano
- Naira 20,000 Kacal Za A Dinga Cirewa A Banki A Kowacce Rana – CBN
Da yake tsokaci kan abin da ya bayyana a matsayin nasarar gudanar da zabukan fidda gwani da aka gudanar a jihohin Anambra, Ekiti da Osun, Buhari ya bayyana cewa zai bar mutane su zabi shugabannin da suke so.
A cewar wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman, Femi Adesina, ya fitar, ya ce mutane su zabi wanda suke so a kowace jam’iyya.
“Ba za mu bari wani ya yi amfani da kudi da ’yan daba don tsoratar da jama’a ba.”
Ya kuma bayyana ra’ayinsa na cewa zabe ya fi wuya a yi magudi a yanzu, domin a yanzu ‘yan Nijeriya sun fi sanin alfanun tattaunawa ya fi daukar makamai.
A wani lamari makamancin haka, shugaban kasar ya karbi tawagar shugabannin siyasa, addini da ‘yan kasuwa daga Jihar Gombe wadanda suka ziyarce shi a ofishinsa, domin nuna jin dadinsu kan rawar da ya taka wajen gano man fetur a yankin Kolmani na jihar.
Da yake yi wa maziyartan jawabi, Buhari ya ce duk da irin abubuwan da masu sukarsa za su ce gwamnatinsa ta samu ci gaba wajen daidaita al’amuran tsaro a kasar nan, farfado da tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa.
Shugaban da ya bayyana ziyarar a matsayin kara karfafa gwiwa, ya ce yana gudanar da aikinsa ne kawai.
Shugaban ya bayyana cewa, ya yi aiki a matsayin Ministan Man Fetur na sama da shekaru uku a 1970, an yi nazarin yiwuwar yin aiki, yana mai imani zai kara daidaita harkokin siyasa, don haka ga man fetur, ya kamata a taya shi murna.
A halin da ake ciki, Gwamna Mohammed Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya bada tabbacin cewa aikin zai bunkasa tattalin arzikin kasa, samar da ayyukan yi, da kuma amfanar manoma.