Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba zai tsaya takara ko ya nemi wani muƙami na siyasa a zaɓen 2027 ba, inda ya ce shiga siyasar sa a yanzu don tallafa wa nagartaccen jagoranci ne kawai, ba don wata buƙata ta kansa ba.
El-Rufai ya yi wannan bayani ne a Kaduna yayin da yake tarɓar wasu ƴan jam’iyyar PDP da suka sauya sheƙa zuwa ADC ƙarƙashin jagorancin Aliyu Bello. Ya ce tun bayan barin mulki a 2023, burinsa shi ne ya nesanta kansa daga siyasa, amma halin da ake ciki ne ya sa ya sake shiga domin ya taka rawa ta goyon baya.
- Sadiq Umar Da Bello El-Rufai Sun Sayi Ƙungiyar Rancher Bees FC Ta Kaduna
- ADC Tana Da Damar Kayar Da Tinubu A Zaɓen 2027 – Amaechi
A cewarsa: “Wannan gwamnati babu abin da take yi sai ƙarya kullum. Ni ba zan tsaya takara ba. Ba na son zuwa majalisa. Ba zan tsaya neman wani muƙami ba. Abin da nake so shi ne mu haɗa kai mu kawar da azzalumai.”
El-Rufai ya ƙara da cewa a yanzu hankalinsa ya fi karkata wajen ba matasa, da mata, da masu kishin gyara dama su shiga harkokin siyasa. Ya kuma yi kira ga matasan Kaduna su yi rijistar katin zabe domin samun damar zaɓar shugabannin da suka cancanta, yana mai nuna damuwa cewa yayin da Lagos da Osun suka yi rijistar mutane 600,000, Kaduna ta yi 60,000 ne kawai.
Ya jaddada cewa dalilin da ya sa ya dawo cikin siyasa shi ne kishin ganin an samu jagoranci nagari a Nijeriya, ba wai don neman muƙami ko wani muradi na kansa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp