Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jadadda aniyarsa na kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a Nijeriya.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da hadimin Buhari, kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi.
- Buhari Ya Taya Amusan Murnar Lashe Zinari A Gasar Tsere Ta Duniya
- Zamu Hukunta Duk Wanda Ba Musulmin Ba Da Ya Sake Keta Harami – Saudiyya
Shehu ya ce manyan hafsoshin tsaron kasar nan iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen matsalar ‘yan bindiga a Nijeriya.
Ya kuma jajanta wa tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Adamu Muazu, saboda kashe dan uwansa da ‘yan bindiga suka yi tare kuma da sace ‘yar uwarsa.
Yayin da yake bayyana ‘yan bindigar a matsayin makiya al’umma, shugaba Buhari ya ce ya kadu matuka da wannan kisan.
Ya kara da cewa ”Na yi matukar kaduwa da jijn labarin kashe dan uwanka, tare da kama ‘yar uwarka. Wannan masifa kullum karuwa take yi a kasar nan. Na sani kuna cikin halin damuwa, ina taya ku bakin ciki”
”Matsalar tsaro ita ce babban abin da na sa a gaba, na kuma umarci manyan hafsoshin tsaron kasar da su yi iya bakin kokarinsu, domin kawo karshen wannan matsala da kasarmu ke ciki”. In ji Buhari
Kalaman na Buhari na zuwa ne biyo bayan wani bidiyo da minti 10:11 da ‘yan bindiga suka saki a ranar Lahadi, inda aka nuna su suna azabtar da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da suka sace a watan Maris.
‘Yan bindigar sun yi barazanar sace Buhari da kuma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.