Ezenwo Wike, ya sake nanata cewa, shi fa ba zai taba shiga cikin jam’iyyar APC ba, duk kuwa da cewa ya ba wa gwamnoninta da suka fito suka yi tsayuwar daka wajen ganin cewa dan takarar shugaban kasa ya fito daga shiyyar kudu a karkashin APC din.
Ya bayar da misalai kan batutuwan da suke yaduwa cewa zai koma cikin APC cewa labarin kanzon kurege ne, ya ce, har yanzu shi cikakken mamba ne a jam’iyyar PDP.
- Akwai Wasu Kusoshi A Fadar Shugaban Kasa Da Ke Goyon Bayan Atiku – Wike
- Wike Ya Soke Ba Wa Atiku Filin Wasa Na Ribas Don Gudanar Da Yakin Neman Zabe A Jihar
Gwamna Wike wanda ya bayyana haka a ranar Litinin yayin taron ganawa da majalisar sarakuna na zango-zango da ya gudana a Fatakwal babban birnin jihar.
Ya shelanta wa majalisar sarakunan cewa a zaben shugaban kasa da zai gudana ranar Asabar mai zuwa, zai zabi dan takarar da zai tabbatar ya hada kan al’umar kasar nan ne ba wanda zai farraka su ba.
Ya ce: “Ni ba mambar jam’iyyar APC ba ne kuma ba zan taba zama haka ba amma, sun nuna min cewa su jarumai ne a kasar nan saboda gwamnonin sun fito balo-balo sun ce a tsaya a duba hadin kan kasar nan, dole shugabancin kasa ya tafi Kudu.
“Gwamnonin APC sun ce bisa yadda kasar nan take tafiya, suna son hadin kai, saboda haka shugaban kasa dole ya fito daga kudu.”
Da ya ke magna kan rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP, Wike ya bayyana cewar jihar Ribas ta bada gudunmawa sosai wajen daurewar PDP tun daga zamanin mulkin tsohon gwamna Dakta Peter Odili har zuwa gwamnatinsa.