Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ba zai yi ƙasa a gwuiwa ba yayin da yake da niyyar sauya salon da zakarun na gasar Firimiya suke yi a halin yanzu domin ganin sun dawo cikin hayyacinsu duba da cewar sun kwana biyu ba tare da ɗanɗana daɗin nasara a wasannin baya bayan nan da suka buga ba.
City wacce ta lashe kofunan Firimiya shida cikin shekaru bakwai da suka gabata, ta samu nasara sau 1 a wasanni 13 da ta yi a baya, inda ta yi rashin nasara a wasanni tara, hakan dai ya jefa Guardiola cikin matsanancin matsin lamba, amma ya sha alwashin ba zai zargi wani daga cikin yan wasansa ba.
- Yadda Wasan Manchester Derby Ya Kaya A Etihad
- Maguire Na Son Sabunta Kwantiraginsa A Manchester United
“Ba zan yi ƙasa a gwiwa ba, ina so in kasance a nan kuma in juya abubuwa ba kamar yadda suke a halin yanzu ba,” inji shi a wata hira da ya yi da manema labarai kafin wasansu da Leicester City a yau Lahadi, ina ganin dukkanmu a aikinmu muna son yin abin da ya dace kuma mu faranta wa jama’a rai, wannan ba abin musantawa ba ne.
Ya cigaba da cewa mun san cewar yan wasanmu na ɗauke da raunuka iri iri amma wannan ba dalili ba ne da zai sa mu kasa taɓuka abin azo a gani a wasanninmu, saboda haka akwai buƙatar mu sauya salo domin samar da sakamako mai kyau a nan gaba.